✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka kama jami’an tsaro za su kai wa ’yan bindiga N60m

An kama su da tsabar kudi N60m a kan hanyarsu ta zuwa maboyar ’yan bindiga

Dubun wasu jami’an tsaro ta cika a yayin da suke kan hanyarsu ta yi wa ’yan bindiga jigilar kudi Naira miliyan 60 a Jihar Kaduna.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta ce an cafke su wadannan jami’an tsaro da ba a bayyana ba ne a lokacin da suke kai wa ’yan ta’addar kudin a matsayin kudin fansa.

PRNigeria ta ambato wani jami’in tara bayanan sirri yana cewa, “An kama tsabar kudi N60,000,000 da kuma motoci da man fetur da muggan makamai da wayoyi a lokacin samamen,” da sojoji suka kai.

“Yanzu haka za mu tura jami’an tsaron da aka kama suna yi wa ’yan ta’adda dakon kudaden zuwa hukumar tsaro ta DSS da kuma Hukumar Tara Bayanan Sirri ta Tsaro (DIA) domin a ci gaba da bincike,” a cewarsa.

Sojojin kasa da jiragen yaki sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri, inda suka yi nasarar hallata wasu daga cikin ’yan ta’addar a maboyarsu, suka kuma kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Majiyar ta ce a lokacin samamen, dakarun soji daga Rundunar Sojin Sama ta 271 da ke Birnin Gwari tare sojojin kasa da ke Gwaska, duk a Jihar Kaduna, sun kubutar da mutum sama da 20 da aka yi garkuwa da su daga hannun ’yan bindiga.

Yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa dai ya zama wata babbar kasuwanci ga ’yan ta’adda, musamman a yakin Arewacin Najeriya, duk kuwa da fadi-tashin da jami’an tsaro ke yi na ganin bayan matsalar.

A baya-bayan nan, lamarin ya yi kamari sosai a Jihar Kaduna, inda kimanin mako biyu da suka gabata, ’yan ta’addar suka dasa bom a kan layin jirgin kasa, suka kayar da wani jirgi da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, suka kashe fasinjoji, suka jikkata wasu, sannan suka yi awon gaba da sama da mutum 40.

Daga Sagir Kano Saleh, Aliyu Jalal da Dalhatu Liman.