✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kama jagoran ’yan bindigan Abuja a Nasarawa

Samaila Wakili Fafa wanda aka fi sani da Habu Ibrahim, shi ne mutum na biyu da ake nema ruwa a jallo a Abuja.

’Yan sandan sun kara kama wani jagoran masu garkuwa da mutane, wanda ake nema ruwa a jallo a Abuja, mai suna Samaila Wakili Fafa.

Samaila, wanda aka fi sani da Habu Ibrahim, shi ne mutum na biyu da ake nema ruwa a jallo a Abuja.

Ya ce, “wanda ake zargin yana daya daga cikin mashahuran masu garkuwa da mutane biyu da Ministan Abuja, Nyemso Wike, ya sanya kyautar Naira miliyan 20 idan aka kamo su da rai ko a mace.

“Dayan kuma, Sa’idu Abdulkadir, wanda ake kira da Dahiru Adamu, an kama shi tun da farko, kuma yana hannun rundunar,” in ji Kwashinan rundunar, Benneth Igweh.

Ya shaida wa manema labarai a ranar Talata, cewa an kama Habu Ibrahim ne a samamen da rundunar ta kai twa maboyar ’yan bindiga a dajin Sadauna da ke Jihar Nasarawa.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya kitsa tare da aiwatar da wasu sace-sacen mutane a Abuja da kewaye.

Ciki har da sace wani Barista Chris Agidy, mai taimaka wa Sanata Ned Nwoko a fannin shari’a da kuma yankin Hakimin Ketti, Sunday Yahaya Zakwai.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa dan bindigan ya jagoranci ’yan sandan zuwa inda aka binne gawar Barista Chris Agidy, inda aka ciro ta aka kai asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada.