Sarkin Fawa na Kasuwar Tudun Wadan Zariya, Abdullahi Ibrahim Bilal, ya tsallake rijiya da baya, bayan wani matashi ya yanke shi da wuka a makogwaro a masallaci.
Matashin da ake wa lakabi da Mugu Ba Shi Da Kama ya nemi yi wa Sarkin Fawan yankan rago, har ya yanke shi da wuka a wuya, bayan idar da Sallar Subahi a ranar Juma’ar da ta gabata.
SAURARI: Halin Ni-’Ya-Su: Wa Ya Kamata Ya Jikan ’Yan Gudun Hijira?
- Limami ya maka jikansa a kotu kan kwace masa mata
- An ware biliyan 4 don zuba mai a motocin ’yan sanda
Mugu Ba Shi Da Kama ya shiga masallacin ne tsirara rike da wata wuka da ya yi amfani da ita ya yanki shugaban mahautan.
Mutanen da ke cikin masallacin sun yi dauki-ba-dadi da matashin, sai da suka yi taron dangi, duk da haka da kyar suka ci karfinsa, har aka kwace wukar.
– Abin da ya faru
Aminiya ta ziyarci basaraken wanda ya shaida mata yadda lamarin ya faru.
“Sunana Abdullahi Ibrahim Bilal amma saboda da sarauta ana kira na Sarkin Fawan Kasuwar Tudun Wada Zariya, kuma kimanin shekara 20 ke nan ina rike da sarautar.
“Wato abin da ya faru shi ne a ranar Juma’a bayan idar da Sallar Asuba ina zaune a cikin masallaci ina lazimi sai wani dan aikena ya zo masallacin, to da ya zo ya fara tsayawa a waje ne kafin ya shigo ciki.
– Yankan rago zai yi min
“Ashe tsirara yake daga shi sai mayafi da ya lullube jikinsa da shi kuma ashe yana dauke da wuka a hannunsa, don haka ko da ya shigo cikin masallacin sai kawai ya dadumi wuyana ya rike kaina da karfi kamar zai yanka dabba yaja wukar.
“Nan take sai Allah Ya ba ni sa’a na rike hannun da wukar take tam, ina daga kwance muna ta kokawa har dai jama’a da suka rage a masallacin suka fara fahimtar halin da muke ciki ni da shi sannan aka kawo mun dauki.
“Daga nan mayafin da ke jikinsa ya fadi sai ya koma tsirara kamar yadda ya zo duniya, aka fara dambe da shi don a kwace wukar da ke hannunsa amma hakan ya so ya faskara.
“Duk da jini da ke zuba a jikina sakamakon raunin da ya ji min, amma haka nan na sake rungumar sa ta baya na kankame shi sannan fa aka samu aka kwace wukar.
“Yaran mahauta suka taso da duka suna neman hallaka shi, da kyar aka hana su, Allah Ya taimake mu aka dauko shi zuwa ofishin ’yan sanda tare da wukar da aka kwace a hannunsa, ni kuma daga nan aka garzaya da ni asibiti don duba lafiyata.
“To a sanina yaron ba shi da wata matsala ta tabuwa sai dai ko ta shaye-shaye, domin ai danmu ne muna tare da iyayensa, kuma a tarihinsa bai taba ciwon hauka ba.
“Kuma kamar yadda na fada ma, da farko cewa yaron aikina ne, Allah Ya hore min shi kuma yana jin maganata, kusan shi nake aike ko’ina, don haka na san shi kwarai da gaske,” a cewar Sarkin Fawa.
Ya kara bayyana wa Aminiya cewa yana zargin wasu abokan sana’arsa mahauta ne suka sa yaron ya hallaka shi, amma ya ce bincike ne kawai za iya tabbatar da gaskiyar lamarin.
A halin yanzu Mugu ba shi da kama yana tsare a ofishin ’yan sanda na Tudun Wada inda ake bincikar sa, shi kuma Sarkin Fawa ya koma gida bayan an sallamo shi daga asibiti.