✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kai wa Fulani hari a Oyo

Ana neman Sunday Igboho, jagoran wadanda suka kai wa Fulani harin

An kashe wata matar arue da ’ya’yanta biyu a harin da matasan Yarbawa suka kai wa Fulani a yankunnan Iganga, Ibarapa ta Arewa na Jihar Oyo.

An kai wa Fulanin hari ne a ranar Juma’a bayan wa’adin kwana bakwai da wani mai suna Cif Sunday Igboho ya ba su na bar yankunan ya kare.

Matasan da Sunday Igbohon ya jagoranta zuwa al’ummomin Fulanin sun fi karfi jami’an tsaro da aka girke a kusa da al’ummomin, suka rika kashe-kashe da kona gidaje da motoci.

Daya daga cikin gidajen da matasan suka lalata suka kum banka masa wuta.

‘Ba mu san halin da iyalanmu ke ciki ba’

Sarkin Fulani, Alhaji Salihu Kadiri, ya tabbatar wa Aminiya daga inda yake buya cewa maharan sun kona fadarsa da gidaje da dama, “yanzu haka, ina boye ne a cikin daji.

“Mun tsere ne domin kubutar da rayuwarmu bayan mun samu labarin harin. Sun kone motocina da na ’ya’yna.

“Sun kuma kashe wata tsohuwa da nake kyautata zaton matata ta fari ce.

“A halin yanzu ba zan iya ba da cikakken bayanin abin da ya faru da mutanenmu ba da aka kashe saboda yar yanzu muna wuraren da muka bobboye ne,’’ inji shi.

Day daga cikin ’ya’yansa, Aliyu Salihu Kadiri, ya shaida mana ta waya cewa an kashe mutum uku a harin da aka kai.

“Sun kona unguwanninmu. Babbar damuwarmu ita ce mata da kananan yara da tsoffi da ba za su iya guduwa ba”, inji shi.

Wani mazaunin mai suna Mustapha Aliyu Moddibo, ya ce al’ummomin Fulani da ke yankunan na cikin hadari.

Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Reshen Jihar Oyo, Alhaji Ibrahim Jiji ya bayyana takaicin abin da ya faru, tare da kiran Gwamnati da ta kawo dawwamammen karshe ga rikicin Fulani da manoma a Jihar.

Wasu motocin da matasan Yarabawan suka kona a lokacin harin

Ba fada ya kai mu ba —Igboho

Wani mai magana da yawun Cif Sunday Igboho, da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa ba da yawun maigidansa aka yi barnar ba.

Ya ce babu mamaki abin da ya faru ya kasance ne bayan Sunday Igboho ya bar Igangan.

“Sunday Igboho ya je ne ba don fada ba, ya je ne don ya ba wa bangarorin baki da kuma tabbatar wa Yarabawa cewa ba a samu matsala ba.”

Rundunar ’Yan Sanda

Mun tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, Oluwagbeniga Fadeyi,  kuma ya yi alkawarin binciko abin da ya faru sannan ya waiwaye mu.

Sai dai har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto, ba mu samu jin ta bakinsa ko irin bayanan da ya tattaro ba.

Ana neman Sunday Igboho

A hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya umarci Kwamishinar ’Yan Sandan Jihar Oyo,m Ngozi Onadeko, da ta tsare Sunday Igboho.

Shi ma Gwamna Seyi Makinde na Jihar ya umarci Kwamishinar ’Yan Sandan da ta kamo Igboho wanda shi ne ya ba wa Fulani wa’adin kwana bakwai su bar yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Gwamna Makinde ya ce ba zai lamunci fakewa ba da sunan kare Yarabawa ba ana haddasa rikicin kabilanci a jihar.

Makinde ya ba da umarnin ce bayan Igboho ya sake barazana cewa dole Fulani su bar kasar Yarabawa saboda zargin su da hannu a garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka.

Gwamnan ya ce yakin Gwamnatin Jihar da hukumomin tsaro ke yi shi ne na fuskantar masu aikata laifuka ne ba tare da la’akari da kabila, addini ko yanki ba.

Mushen wata dabba da maharan suka kashe.

Ya ce ba zai yarda da duk wani mai yunkurin kawo fitina ko neman hana wani dan kasa zama a jihar ba, domin hakan ya saba wa dokar kasa.

“Masu neman ta da rikicin kabilanci ’yan ta’adda ne, da zarar kun kama su, ku tabbata sun fuskanci hukunci.

“Babbar damuwar gwamnatinmu ita ce tsaro domin duk kyawawan tsare-tsarenmu na tattalin arziki ba zu kai ga nasara ba idan babu tsaro da kwanciyar hankali.

“Saboda haka duk wanda ya yi wanin abin da ya saba wa dokar kasa ba za mu kyale shi ba.

“Ba kuma za su fake da sunan kare Yarabawa ba su rika tayar da fitina.

“Na san bayan zuwanki, kin samu labarin abubuwan da ke faruwa a yankin Ibarapa.

“Ina fada a nan cewa ba Hausa-Fulani muka sa a gaba ba, masu aikata manyan laifuka muka sa a gaba,” inji gwamnan.