Hukumomi da tsagayoyin ilmi a jami’o’i daban-daban a kasar nan sun dauki lokaci suna hannuka mai sanda game da tsangwamar tsuntsaye musamman ungulai wadanda rayuwarsu ke da matukar tasiri ga bil-Adam. Amma duk da haka al’umma ta yi watsi da batun, inda abu ne mai wuya ka ga ungulai ko’ina a kasar nan kamar shekarun baya. Haka kuma tuni wasu suka maida fataucin ungulai wata sana’a ta samun kudi, inda a wata kasuwa a Ibadan an samu wasu mata fiye da 50 da suke kasuwancin saida matattu da rayayyun ungulai. A yayin da aka haramta fatauci da safarar kowadanne irin tsuntsaye kamar kuma yadda babban taron baje koli na duniya ya tsawatar. Tare da haka fataucin ungulai na kasancewa a sarari cikin wasu kasuwannin kasar nan, wasu lokutan a boye, inda ake kulla cinikinsu.
Aminiya ta gano cewa a Kalaba na Jihar Kuros Riba ungulai na yawo cikin lumana, inda ake ganinsu a mayankun dabbobi daban-daban a yankin, sannan cikin adadi masu yawan gaske dake rayuwa saman rufin gidaje da iatatuwa.
Haka kuma ana iya ganin ungulan na walwala a sarari gidan zoo na kasa dake Babban birnin tarayya Abuja, haka nan a garin Ajebo dake Ibadan a Jihar Oyo inda ake ganinsu hatta a cikin keji ana kiwonsu. Ana kuma ganin ungulan a kasuwar ‘Yan Kaji dake Sabon Gari a Kano cikin keji ana sayarwa, duk da yake cinikayyar na gudana ne a boye. A nan Abuja, Shugaban kungiyar Masu Saida Tsuntsaye, Bashiru Sani ya bayyana cewa suna sayar dawasu tsuntsaye a kejim kusa da babban masallacin kasa dake Abuja, inda ya ce a kullum suna samun ungulai daga Legas da Sokoto, inda farashin kowane daya ke kaiwa naira dubu 80. Amma a Fegin-Baza da kuma Sakiya dake karamar Hukumar Tsafe na Jihar Zamfara, inda zaka iske kananan yara da yawa ba su san ungulu ba sam. Haka labarin yake a Giwa na Jihar Kaduna da Argungu a Jihar Kebbi.
Shugaban Dazukan Gwamnati na kasa na Najeriya, Ibrahim Goni, ya dauke mu baya har zuwa shekarun 2000, inda ya ce a lokacin adadin ungulai a kasar nan baa bun da za a yi kuka ba ne, domin suna nan sassa da yawa a kasar nan, amma daga wannan shekarar ta 2000, sai labarin ya fara sauyawa, inda ungulan suka yi batar-dabo aka daina ganinsu. Koda ana ganinsu har a yanzun a wasu sassa na kudancin kasar nan, amma a Arewa labarin ya sha bamban.
Ya ce dalilan da suka haddasa hakan shi ne, har da salwantar inda za su yi shekarsu, sakamakon farauta da sare manyan itatuwa, “Matsalar ma ba ga farautar kadai ta dogara ba, har ma da sare itatuwa barkatai. Domin a duk lokacin da aka sare itatuwan da shekar tasu ke kai, to babu sauran damar da aka ba su na ci gaba da rayuwa a wannan wurin. To anan dole ne su yi kaura zuwa wani wurin daban, a kuma hanyar neman wani wurin ne suke gamuwa da hadura da yawa, za a iya farautarsu, za a iya kama su, sannan za su iya mutuwa. Bugu da kari babban hanyar da tafi karar da ungulai ita farauta don abinci ko don saida sassan jikinsu saboda magungunan gargajiya na al’ada.”
Wani sanannen mai maganin gargajiya a Kano, Malam Zubairu Wada, ya shahara wajen sayar da magungunan gargajiya, ya bayyana cewa, “Babu yadda za a yi su daina wannan kasuwanci na saida sassan ungulu ko kwansa, musamman ga mutanen da suka yi imani da samun kudaden tsafi. Kuma ina tabbatar maka cewa ana shigo da kan ungulu kimanin 150 a duk wata nan Kano daga Senigal da Ghana a duk wata. Abinda ke nuni da cewa kimanin kan ungulai dubu 180 ake shigowa da su Kano duk shekara.
Jami’i a Sashen Harhada Magunguna da Binciken Sinadaran kwayoyin Halitta na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Dakta Aminu Musa ya ja hankalin al’umma game da bacewar shekar ungulu tsawon lokaci a Zariya.
Haka kuma ya yi nuni bisa yadda itatuwan Rimi suka yi batar-dabo a Zariyar, wadanda Tsohon Sarkin Zazzau, Marigayi Aliyu Dan Sidi ya sha gwagwarmayar dasawa a gefen tituna, “amma a zamanin mulkin soja na Janar Babangida a lokacin da aka fara gina tagwayen hanyoyi, sai aka rika sare itatuwan. Aikin tagwayen hanyoyin, wanda ya faro tun daga Gadar Kubani har zuwa cikin birni.
“A yayin da itatuwan Rimi da na Maje kalilan suka tsira daga wannan aikin, amma a wancan lokaci idan ka shigo Zaria, babu abinda zaka rika tazali da shi sama da wadannan itatuwan gwanin ban sha’awa. Sannan wani karin abin burgewa shine idan ka bi tsawon hanyoyin, inuwar itatuwan ne za su rika yi maka jinka ta dukkan kusurwowin, kana kuma ungulai na watayawa bisa ganyanyakin itatuwan, amma fara wannan aiki ke da wuya duka wannan ya zama tarihi. Kai ina jin ma zan iya cewa babu sauran wata itaciyar Rimi yanzu haka a Zariya.”
Haka shi ma Dakta Dauda Tanko na sashen kimiyyar halittu na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Lokoja ya ce; “Zaka ga daruruwan ungulai bisa kan itatuwan Rimi, wadanda suka yi wa hanyar da ta taso tun daga Fadar Sarkin Zazzau ta ratsa ta cikin birni har zuwa Tudun Wada suka dangana da Samaru. Ilahirin hanyoyin sun samu tagomashin wadannan itatuwa na Rimi gwanin ban sha’awa,”
“Ga dabi’a su wadannan tsuntsaye na bukatar itatuwa masu tsawo masu kuma kaurin ganyaye ta yadda za su reni ‘ya’yansu, amma a yayin da aka rasa wadannan itatuwan, wadanda al’umma suka sare ko aka tunbuke su, to sai su fantsama zuwa neman inda za su yi sheka don renon ‘ya’yansu kanana,” a cewarsa.
Masanin kimiyyar halittun ya ci gaba da kawo mafita ga irin wannan aika-aikar; “Babban abin da ya kamata mu yi shi ne, mu dakatar da aikata abin da mu ka san ba daidai ba ne, misali; idan mun kasance muna farautar wadannan ungulai, idan mun san muna cutar da su, to wajibi ne mu daina, sannan mu kirkiri hanyoyin wayar da kan al’ummarmu bisa wannan mummunar dabi’a, a sannan ne mutane za su fahimci alfanun rayuwar wadannan tsuntsaye a tsakaninsu.
“Yana da matukar fa’ida mu yi haka nan, sannan a yayin isar da sakon ya dace al’ummarmu su fahimci amfanin rayuwar tsuntsaye irin Ungulu a tsakaninmu, duk abinda ka gani akwai hikima da dalilin faruwarsa, hakika muna bukatar wadannan tsuntsaye a tsakaninmu don karkon rayuwarmu, al’amura suna gurbata idan aka rasa tsuntsaye masu kima a tsakanin al’umma irin ungulu kamar yadda tabbatattun binciken duniya a yau suka nuna.
“Bincike ya tabbatar da cewa ungulu su ne tsuntsayen da ke kauda kimanin kashi 99.9 na kwayoyin cuta da bakteriya da sauransu a tsakanin al’umma, sannan su ne jami’an kai daukin gaggawa. Don haka idan aka rasa su, cututtuka da dama za su rasa mai kauda da su, sannan za su rika girma har su zama wata annoba ta daban. Domin ungulu tana fada da kwayoyin cutar carcass kafin ta rika zuwa bakteriya da sauran cutaka irinsu microbes da sauransu, su kuma wani abin mamaki cutukan ba su iya masu illa, saboda an halicce su da wannan kariyar. Da wannan sai suka zama ma su zuke kwayoyin cutuka irin su microbes su ajiye a cikin jikinsu ba tare da ya illa ta su ba, sannan su kubutar da al’umma daga sharrin hakan,” in ji shi.
Tsohon Shugaban Jami’ar Ile-Ife dake Jihar Osun, Farfesa Wande Abimbola ya bayyana cewa ko kadan yankin Yarbawa ba su cutar da ungulu, don haka ungulan suka watayawa ko ina a yankin, “Ungulai na nan birjik a yankin Yarbawa suna rayuwarsu babu tsamgwama. Domin ungulu tsuntsun alfarma ne kuma haramun ne kisan su haka siddan a al’ada. Haka kuma mutane ba su cin ungulu kmar yadda ba su kashe su bisa ganganci. Ungulu na da dadadden tarihi kuma al’ummar yarbawa sun dauki ungulu da muhimmanci tun fil-azan. Kuma akwai wani imani da ‘ya’yan sarkin Ila Orangun suka yi da ungulu game da rayuwarsu, wanda har ake al’amuran neman sarauta da su a wancan lokaci.” Aminiya ta gano cewa hatta a fadar basaraken gargajiya na Idanre a Jihar Ondo ungulu na da matukar tasiri.
Har ila yau, wani masani a sashen harsunan Najeriya da Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Adamu Malumfashi ya yi karin haske game da rashin tasirin ungulu a kasar Hausa musamman a cikin Karin maganganu ko tatsuniyoyinsu, wadda na san da yawa daga cikin tatsuniyoyi kasancewar na taso ne a kauye, inda a al’ada lokacin da muke kanana a makarantun furamare ana yi mana tatsuniyoyi daban-daban amma da wuya ka ji na ungulu, ba wai ina nufin babu ba ne, amma dai ni ban ko daya ba,” a cewarsa.
Game da bacewar ungulu ko raguwarsu a kasar nan, Mista Abimbola ya ce, “A lokacin da nake karami na taso a fadar sarauta a Jihar Oyo, zaka iya tafiyar kusan mil guda a daji, amma da wuya ka iya ganin rana. Kasancewar itatuwa da sauran tsirrai ke tokare sararin samaniya a bisa kanka. Irin wannan yanayi ne ya baiwa Ghana damar samar da Cocoa a shekarun 1930, to a lokacin ne kuma mutanen Ibadan suka bazama shuka cocoa. Daga bisani a shekarun 1940 zuwa 1950 ya watsu zuwa Oyo, Ekiti, Ijebu da sauran wurare a yankin. Cikin karni guda muka sare kusan dukkan itatuwan da muke da su, amma da ace bamu yi rububin shuka cocoa din ba, da yanzu itatuwan namu na nan daram. Sannan dalili na biyu shi ne, samar da katako ta hanyar sare itatuwa sannan a dauke su zuwa kasashe irin su Turai, wadannan su ne manyan dalilan da suka haddasa bacewar dazukanmu masu cike da tasiri a yau.”