Wasu Manoma a Karamar Hukumar Billiri a Jihar Gombe sun bayyana wa Aminiya jin dadinsu kan yadda suka samu habakar amfanin gona a daminar bana sakamakon koyi da dabarun noma da suka yi daga shirin Sasakawa.
Manoman sun samu wannan tallafin ne a karkashin shirin Noma da Sasakawa suka bullo da shi da hadin guiwar Hukumar Aikin Gona ta Jihar Gombe, don ganin an bunkasa noma daga kanana zuwa matsakaita da manyan manoma.
- Zanga-zangar Zakzaky: IMN ta maka Shugaban ’Yan Sanda a kotu
- Tsoho ya kashe daliban jami’a 5 bayan ya yi mankas da giya
- An haramta lodin mutane a motocin daukar dabbobi
Wasu daga cikin manoman sun jinjina wa shirin a wata rana da shirin ya ware mai taken ‘Media Field day’ da suka shirya don nuna aikace-aikacen da suka gabatar a ranar Talatar da ta gabata a garin Billiri a Jihar Gombe.
Da yake bayyana wa manema labarai yadda suka ci gajiyar shirin, Shugaban Kungiyar manoma ta Kalkwi-Ka’amdo da ke kauyen Amtawalen, a garin na Billiri, Yahaya Amuga ya ce, sun samu yabanya a daminar bana sabanin sauran shekaru da suke yi noma kafin zuwan shirin Sasakawa.
Ya ce, tunda suka rungumi wannan tsari na noma irin na Sasakawa matsakaicin manomi yana iya samun buhu 30 a kadada daya ba kamar a baya da suke samun buhu 10 zuwa 15 ba, inda ya ce ba wani abu ne ya jawo haka ba illa samun horo da suka yi na sabon tsarin noma na ‘Good Agricultural Practices (GAP)’.
“Manoma sun samu irin shuka mai inganci, sun samu horo kan yadda za su yi shuka, su zuba taki da kuma maganin feshin kwari yadda ya dace a karkashin shirin.
“Mun ji dadi matuka na yadda muka samu karin kudin shiga ta wannan noma da muke yi” in ji shi.
Amuga ya kuma bayyana ambaliyar da ta auku a matsayin babban kalubale da ya mayar musu da hannun agogo baya, domin ta shafe musu wasu gonaki masu yawa a wannan yanki nasu.
Sannan ya roki gwamnatoci a dukkan matakai da su kawo musu dauki domin su samu damar yin noman rani ko za su mayar da gurbin asarar da suka yi a lokacin damina.
Har ila yau, ya roki shirin na Sasakawa ya samar musu da injinan casar masara da na shinkafa domin sarrafa amfanin gonar da suka noma domin rage musu asara a harkar nomansu.
Ita ma wata manomiya kuma Shugabar Kungiyar Mata Manoma, Misis Abigail Eli ta ce, mata ma ba a bar su a baya ba a harkar noma, wanda yanzu haka su ma sun rungumi dabarun noman zamani Misis Eli ta ce, wannan tallafi ya inganta harkokin nomansu da kuma bunkasa musu tattalin arziki.
“Mu ma mun samu horo kan sarrafa abinci mai gina jiki daga abubuwan da muke nomawa don samar da abincin gargajiya,” in ji ta.
Ta kara da cewa, mata da yawa sun koyi yadda ake sarrafa madarar waken soya da awara da dambun zogale da na rama daga abubuwan da suke nomawa daga waken soya da sauransu.
A cewarta, wannan tallafi ya mayar da duk matan karkarar masu sana’o’in da suka dogara a kansu suke kuma tallafa wa mazajensu.
Sannan sai ta roki shirin da ya samar musu da injin markade don kungiyar ta samu karin kudin shiga ta yadda za ta rika markada kayayyinsu ba tare da sun kai wani waje suna biyan kudi ba.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Manoma da Hadin Kai ta Sainsai, Malam Ayuba Hamma ya shaida wa Aminiya cewa, manoma sun riga sun zama manajoji na sanin irin tazarar da ake so a bayar tsakanin shuka da shuka don samun yabanya saboda dabarun noma da aka koyar da su.
A cewarsa bisa ga yadda harkokinsu suka bunkasa, yanzu haka a kungiyarsu na iya ba da rance marar ruwa ga mambobinsu domin su samu damar bunkasa nomansu.
“A lokacin girbi muna girbe amfani mai yawa da muke kai wa kasuwa, wanda hakan yake taimaka wa mambobinmu cikin sauki” in ji shi.
A nasa bangaren Mista Isaac Eni, Shugaban Sashin Wayar da Kan Manoma Harkar Kasuwanci na Sasakawa cewa ya yi, wannan shirin yana taimaka wa manoma da injin casa da na zazzabar shinkafa da injin markade da sauran abubuwa don taimaka musu wajen kara samun kudin shiga a harkokinsu na kasuwanci.
Mista Isaac ya kara da cewa, injinan ba kyauta za su dinga ba su ba, rance ne a farashi mai rangwame da za su biya cikin shekaru biyu ko uku ba tare da sun ji zafin biya a dunkule ba.