✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NYSC ta hana masu yi wa ƙasa hidima shiga sansanin horo a Kano

Matasan sun roƙi hukumomin da abun ya shafa su taimaka musu.

Wasu matasa masu shirin yi wa ƙasa hidima (NYSC) sun maƙale a sansanin Kusalla da ke ƙaramar hukumar Ƙaraye a Jihar Kano.

Ɗaya daga cikin matasan, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an hana su shiga sansanin ne saboda sun zo da yamma.

Ya bayyana cewa da yawan waɗanda abin ya shafa sun fito ne daga Yankin Gabas da kuma Kudanci ƙasar nan, kuma sun fuskanci matsaloli a hanya kafin isowarsu sansanin.

“Abun takaici ne yadda muka sha wahala kafin zuwa nan, amma a hana mu shiga. Wasu daga cikinmu sun samu takardar shiga sansani a ƙurarren lokaci, kuma sun yi tafiya tsawon kwanaki biyu ko uku kafin su iso Kano,” in ji shi.

“Yanzu mu kusan 100 mun maƙale a man, muna nan ba tare da mun san makomarmu ba.”

Wani matashi, shi ma ya faɗi irin matsalar da ya fuskanta, inda ya ce, “Na iso Kano ranar Alhamis, rana ta biyu da aka fara shiga sansani. Motarmu ta samu matsala a hanya, kuma ban iso Kano ba sai ƙarfe 1 na dare. Dole muka kwana a hanya. Washegari kuma wayata ta lalace, kuma duk takarduna a ciki suke, don haka sai na je na gyara wayar, wanda ya ɗauke ni tsawon wani lokaci.

“Daga ƙarshe na iso sansanin da ƙarfe 11 na dare, amma lokacin duk sun yi barci, babu wanda zai karɓe mu. Mun samu labarin cewar wasu sansanoni sun ci gaba da yin rajistar ɗalibai har cikin dare.”

Ya ƙara da cewa, “Yanzu sun bayyana mana cewa an rufe shafin rajistar daga Abuja. Wasu daga cikinmu ba su da kuɗin da za su ci abinci. Wasu daga cikin matan da ke cikinmu sai kuka suke yi. Muna buƙatar taimako sosai.”

Matasan da ke shirin yi wa ƙasa hidima, suna roƙon hukumomin da abin ya shafa su kai musu ɗauki saboda suna halin rashin tabbas.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin NYSC a Kano, Juliana Nahemiah, ya ci tura saboda ba ta ɗaga kiran waya ba.