Kwana 26 da sace daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina a Jihar. Neja, har yanzu babu wani sashin labari kan makomar daliban.
Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa hukumomi a Jihar sun ja kunnen iyaye da da malamai da ma mazauna yankin kan kada su kuskura su sake hira da ’yan jarida kan ceto ’ya’yan nasu.
Kafin faruwar lamarin dai mazauna garin na Tegina da ke da makwabtaka da garin Zungeru da Kagara, shalkwatar Karamar Hukumar Tafa kan gudanar da harkokinsu ba dare ba rana.
To sai dai labarin ya canza tun bayan da aka sace daliban ranar wata Lahadi, 30 ga watan Mayun 2021.
Lamarin dai ya jefa tsoro da zullumi a zukatan mazauna garin, kasancewar yanzu akasarinsu su kan rufe shagunansu su tafi gida da zarar an idar da Sallar Isha.
Baya ga harkokin kasuwanci, al’ummar garin wadanda akasarinsu manoma ne sun ce basa iya zuwa gonakinsu saboda fargaba, suna masu cewa hakan na barazanar kawo yunwa a yankin.
Rahotanni sun ambato Shugaban Islamiyyar, Abubakar Tegina yana cewa, “Ni da idona na ga mutane dauke da muggan makamai a kan babura tsakanin 20 zuwa 25. Sun shiga makarantar sannan suka yi awon gaba da kusan dalibai 150.”
Ko da yake daga bisani wasu daga cikinsu sun sami tserewa daga hannun ’yan bindigar, da dama daga cikinsu har yanzu suna can, yayin da masu garkuwar da su ke neman miliyoyin Nairori tare da barazanar kashesu in bukatarsu bata biya ba.
An hana mu magana da ’yan jarida – Iyayen dalibai
Wakilinmu da ya ziyarci yankin a karshen makon jiya ya rawaito cewa har yanzu iyayen daliban na cike da tsoro da fargaba.
Ko da yake, iyaye da hukumar makarantar da ma masarautar Kagara sun ce an hana su hira da ’yan jarida har sai an kubutar da daliban, wasu daga cikinsu da suka tattauna da Aminiya bisa sharadin ba za a ambaci sunansu ba sun ce suna cikin matsananciyar damuwa.
Daya daga cikin iyayen mai ’ya’ya biyu, mace da namiji ya ce, ”Ina cikin damuwa tun da aka sace min yaran. Amma a matsayina na Musulmi, na mika komai ga Allah.
“Ranar da abin zai faru, ina cikin shagona tare da abokina na hango ’yan bindigar a kan babura sun tunkaro mu. Sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi don su tsorata jama’a kuma kowa ya rika gudun tsira a lokacin.
“Daga nan kai tsaye sai suka wuce makarantar sannan suka yi awon gaba da daliban, ciki har da ’ya’yana da wasu na ’yan uwana su biyu. Ni kaina sai da na gudu gidan wani makwabcina na shiga na buya a cikin rijiya. Sai da suka shiga gidana suna nemana amma basu ganni ba,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga gwamnati kan ta kara matsa lamba wajen ganin ta kwato daliban da ransu.
Sai dai ya yi gargadin cewa idan ba a yi wa tufkar hanci ba, makomar ilimi a yankin na cikin garari.
Ya kuma ce duk da abin da ya faru din, zai ci gaba da tura ’ya’yan nasa makaranta.
Shima wani uba ga daliban wanda bai amince a bayyana sunan nashi ba ya ce lamarin har ciwon zuciya ya sa masa.
Ya ce lamarin ya ritsa da ’ya’yansa biyu, dukkansu maza, kuma har yanzu babu wata cikakkiyar magana tsakaninsa da masu garkuwar, sai dai da wani kwamitin tsaro da aka kafa.
”Sakamakon harin har ciwon zuciya ne ya kama ni. Daya daga cikin ’ya’yan nawa da aka sace ma har ya kammala Firamare kuma ina shirye-shiryen kai shi Sakandire kafin faruwar iftila’in. Ina kira ga Gwamnati ta kawo mana dauki, komai ya tsaya cak a garin,” inji shi.
Mazauna gari na zaman dar-dar
Mutanen garin na Tegina da dama sun ce tun faruwar lamarin, kusan koai ya tsaya cak.
Wata mai shagon sayar da kayayyaki ta ce yanzu haka iyaye da dama ba sa barin ’ya’yansu su je makaranta saboda fargaba.
Ko da yake yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Gwamnatin Jihar Neja kan dalilin hana iyayen daliban hira da ’yan jarida ya ci tura, amma wata majiya daga gwamnatin ta ce an dauki matakin ne da nufin kare su.