A safiyar ranar Sallah Babba ko Karama, Sarkin Zazzau yakan fito da safe zuwa masallacin Idi a kofar Doka tare da hakimansa da sauran ’yan Majalisar masarautar.
Bayan sauka daga masallacin Idi, sai Sarki ya hau doki ya dawo fadarsa.
- Goron Sallah: Muna dab da kawo karshen ’yan ta’adda a Najeriya – Buhari
- Mutum 4 sun mutu sanadiyyar rushewar bene mai hawa 3 a Legas
Bisa al’ada, in Sarki ya hau doki, a gaban shi akwai Sarkin Hawa wanda shi ne ke daidaita tsarin tafiya sannan sai ’yan kwalkwali suna biye a layi.
Daga nan sai Sarkin Bindiga da Sarkin Baka da jama’arsu taho, bayansu kuma sai Dogaran Dawaki, daga su sai Dawakin Zage.
Wadannan wasu dawakai ne farare da bakake wadanda aka dora masu sirdi aka kuma rufe sirdin domin babu kowa a kansu a na janye da su ne kawai. Daga nan sai Masartan Sarki, watau makada da masu Kakaki da Farai da Sauran su biyo baya.
Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna kuma Sarin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci da dukufa da yin addu’o’i don Kawo karshen yawaitar satar mutane da yin garkuwa da su da kuma kashe-kashen gilla da ake yi wa jama’a ta hanyar ta’addanci a wannan kasa.
Ya yi wannan kiran ne a jawabin da ya gabatar na bukin Sallah ga jama’arsa a fadarsa da ke birnin Zariya.
Ya ce lamarin yana da ban tsoro wadda addu’a ce kawai mafita don haka ya ja kunnen jama’a da su kai rahoton duk wani take-taken da ba su gamsu da shi ba ga hukuma mafi kusa.
Sarkin ya kuma gargadi jama’a da su guji saukar bakin da ba su san daha inda suka fito ba saboda halin tsaro.