Rundunar ’Yan Sandan Kano, ta kama wani matashi bisa zargin kashe jami’in tsaron sa-kai a filin Idi yayin hawan sallah ƙarama.
A cewar sanarwar da ’yan sanda suka fitar, matashin mai shekara 20, ya daɓa wa jami’in wuƙa yayin da yake aiki tare da tawagar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, bayan sallar Idi a ranar Lahadi.
- Farashin fetur ya ƙaru sakamakon hana Dangote mai a Naira
- Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi
Haka kuma, wani jami’in sa-kai ma ya ji rauni kuma yana jinya a Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano.
Rundunar ’yan sandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin amsa tambayoyi.
A baya-bayan nan, ’yan sanda sun hana gudanar da Hawan Sallah a Kano, yayin da ake ci gaba da rikicin sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.