✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar da bukukuwan Sallar bana

Daga Salihu Makera da Tijjani Usman Bello, Maiduguri da Sani Gazas Chinade, Damaturu da Umar Akilu Majeri, Dutse da Amina Abdullahi, Yola da Jabiru A.…

Daga Salihu Makera da Tijjani Usman Bello, Maiduguri da Sani Gazas Chinade, Damaturu da Umar Akilu Majeri, Dutse da Amina Abdullahi, Yola da Jabiru A. Hassan, Kano da Nasiru Bello, Sakkwato da Ahmad Kabir, Katsina

Duk da matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa maso Gabas an gudanar da bukukuwan karamar Sallah a Jihar Borno lami lafiya, sai dai Masarautar Borno ta soke bikin Hawan Sallar saboda tsaro, yayin da gwamnatin jihar ta takaita zirga-zirgar ababen hawa a garin Maiduguri da kewaye har na tsawon kwana biyu. Takaita zirga-zirgar ababen hawan ya taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro, sai dai ba kowa ne ya ji dadin dokar ba domin a cewar wasu takaita zirga-zirgar na rage wa Sallar armashi da katse sada zumunta.
Jama’a da dama sun rika taka sayyada daga gidajensu zuwa filayen Idi na tsawon kilomita biyu zuwa uku don gudanar da Sallar Idi, yayin da jami’an tsaro suka tsananta binciken kwakwaf ga matafiya a kafa da Masallatan Idi.
Malam Bukar Kacallah daya daga cikin masu sukar lamirin dokar takaita zirga-zirgar, ya ce “Wannan doka a lokacin bukukuwar Sallah na takaita mana murnar Sallah  da katse sada zumunci. Sai na ji Sallar babu wani armashi, ina shawartar gwamnati da jami’an tsaro su daina kakaba mana dokar domin ba ta haifar da wani da mai ido, ba ta maganin komai.”
A Damaturu ta Jihar Yobe kuwa wasu ’yan mata ’yan kunar bakin wake ne suka kai tagwayen hari a wani masallacin Idi na Phase 1 a hanyar Maiduguri da Unguwar Gwange, hare-haren da suka ci rayukan mutum 15. Tagwayen hare-haren sun so dagula zaman lafiyar da garin ya samu inda ya girgiza jama’a duk da cewa jama’a sun yi ta maza sun ci gaba da zuwa Sallar Idin bayan tashin bama-baman.
Wani mai suna Malam Ali Muhammad ya ce a lokacin da bam na farko ya fashe a masallacin yana gab da isa wurin, kuma shi da sauran jama’ar da ya samu a masallacin hakan bai razana su ba, haka suka yi Sallah domin sun san cewa Allah bai daukar ran bawa sai wa’adinsa ya cika.
Da Aminiya ta tuntubi Babban Limamin Masallacin Idin Ustas Babagana Malam Kyari dangane da faruwar lamarin, ya ce lallai wadanda suka rasu a sanadiyar tashin bama-baman da ma Allah Ya kaddara hakan ne hanyar ajalinsu kuma ba za su taba wuce lokacin ba, ya yi fatan Allah Ya jikansu Ya yafe musu kura-kurensu. Lalamin ya hori jama’a su kula tare da kauce wa shiga tarkon masu aikata mummunan abu domin a gab da karshen watan Ramadan haka ’yan ta’addar suka kai harin bam da bindigogi a wurin da shugaban Majalisar Malamai na kasa na kungiyar Izala ke tafsiri a Jos.
Bayan harin na ranar Sallah, wasu ’yan kunar bakin wake a cikin wata mota kirar Toyota Jeep Highlanders sun ta da bama-bamai a lokacin da ’yan sanda suke kokarin bincikarsu a shingen duba abubuwan hawa da ke wajen garin Damaturu, harin da ya halaka ’yan kunar bakin waken biyarb da ’yan sanda uku.
Wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya ce tsakaninsa da motar ’yan kunar bakin waken bai wuce mota hudu ba, amma da aka fasa bam din sai da motarsa ta girgiza, wurin ya turnuke da hayaki da kura.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Yobe ASP Toyin Gbadegeshin ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce suna da rahoto kan abin da ke cikin motar maharani, kuma ana kokarin bincikar su ne suka ta da bam din ya kashe su maharan su biyar wata mace da ke cikinsu da ba ta mutu ba a lokacin an samu abubuwan fashewa biyar a cikin jakarta kafin ta cika.
A Jihar Bauchi kuwa an gudanar da bukukuwan Sallar lafiya tare da gudanar da Hawan Sallah da na Daba a ranakun Sallar da washegarin Sallah. Hakimai da dagatai da masu rike da sarautun gargajiya sun hawan Sallah a kofar fadar Sarkin Bauchi jim kadan da dawowa daga masallacin Idi, yayin da washegari Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu ya jagoranci hakimai da masu rike da sarautun gargajiya suka kai gaisuwar Sallah ga Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar a gidan gwamnati, inda nan ma aka yi hawa na musamman.
A jawabin Sarkin ya bukaci Gwamnan Jihar ya gyara wasu hanyoyi a cikin garin Bauchi da sassan masarautar inda ya bukaci al’ummar masarauta su ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu tare da mara wa gwamnati don samun ci gaba mai ma’ana.
Gwamna Abubakar ya yi alkawarin bunkasa rayuwar al’ummar jihar duk da karancin kudin da suka iske lokacin da suka zo gadon mulki. Ya ce, har yanzu kudin da ake cewa Gwamnatin Tarayya za ta ba su ba su iso hannunsu ba, amma duk da haka ya kokarta wajen biyan albashin wata biyu ma’aikatan jihar ke bi a kasa da wata biyu da hawansa mulki. Gwamnan ya kai ziyara ga sarakunan Katagum da Misau da Jama’are wadanda suke fama da rashin lafiya inda ya roki Allah Ya gaggauta ba su lafiya.
 A Jihar Jigawa, wakilinmu ya ce fargaba kan rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan ya hana sarakunan jihar Hawan Sallah a Idin karamar Sallah da aka gudanar ranar Juma’ar da ta gabata.
Jigawa mai sarakunan yanka biyar babu wanda ya yi Hawan Sallah a fadarsa kuma wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, hakan ya biyo bayan bayanan da jami’an tsaro suka ba gwamnatin jihar ne na kada sarakunan su yi hawan.
Majiyar ta ce akwai yiwuwar mayakan Boko Haram su yi amfani da wannan dama su kai wa jama’a hare-hare, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta ba sarakunan umarnin kada su yi hawan.
A fadar masu martaba sarakunan Kazaure da Dutse, sarakunan biyu sun umarci talakawansu su yi wa kasa addu’ar zaman lafiya sun kuma bukaci mazauna masarautun biyu su zauna da jama’a lafiya sun kuma gargadi jama’arsu su guji tayar da fitina.
Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Husaini Adamu da yake jawabi a fadarsa ya yi alkawarin ci gaba da ba gwamnati mai ci cikakken hadin kai domin ci gaban jihar da kasa baki daya ya kuma umarci jama’a su ba gwamnatin jihar cikakken goyon baya don ganin gwamnatin ta kai ga nasara.
Daga Yola, gwamnatin Jihar Adamawa ta bukaci sarakunan gargajiya a jihar su ba da goyon baya da hadin kai wajen bayar da rahoton duk wanda aka gani da wani hali na daban ko ake zargi domin magance matsalolin ta’addanci a jihar.
Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Jibrilla Bindow ne ya bayyana haka a gidan gwamnati da ke Yola, lokacin da sarakunan suka kai masa gaisuwar karamar Sallah a ranar Asabar da ta gabata.
Gwamna Bindow ya umarci masu unguwanni da dagattai da hakimai su kama duk wanda ake zargin dan ta’adda ne su mika ga jami’an tsaro.
Ya ce, “Ba za mu ci gaba da neman yadda za a magance matsalolin ta’addanci ba, ba tare da an nemi shawarar sarakuna ba. Za mu yi kokarin sanya mutum 40 a kowace unguwa ko kasar hakimai domin su zamo idanunmu. Mun ba da damar a sanya unguwanni da kauyuka da kananan hukumomi su kama duk wanda yake ta’addanci ko yake yunkurin aikata haka don mika shi ga jami’an tsaro,” inji shi.
Lamidon Adamawa Dokta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa da Sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu da Murum Mbula Cif Jerome Joel Fa da sauran manyan sarakuna sun ce rashin kamanta adalci ne ke haifar da irin wadannan matsaloli na ta’addanci da na Boko Haram, inda suka ce tunda an sanya su a ciki in sha Allahu sauki zai zo ba da jimawa ba.
Lamido Barkindo ya ce magance wadannan matsaloli hakki ne da ya shafi kowa, don haka dole ne a sa lura kuma a kama ko a kai karar wani da mutane ke zargin zai kawo tashin hankali ga hukuma.
Ya kara da cewa duk manyan sarakunan jihar za su fara nemo hanyar magance wadannan matsalolin. “A matsayina na shugaban Majalisar Sarakunan Jihar nan, zan yi kokarin zantawa da sauran sarakuna domin samo mafita da hanya mafi sauki ta magance matsalar tsaro don a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar,” inji shi.
Daga Kano, wakilinmu ya ruwaito cewa an gudanar da bukukuwan karamar Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana duk da kalubalen tsaro da ake fama da shi a arewacin kasar nan.
Ya ce kuma jama’a da dama sun yi kokari wajen yin hidimomi ga iyalansu duk da matsalar rashin kudi da ake fama da shi a wannan lokaci.
A jawabin Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ya bukaci ’yan Najeriya su ba gwamnatin Muhammadu Buhari goyon baya da hadin kai ta yadda za ta aiwatar da kyawawan manufofin da take da su ga kasar nan.
Ya ce yi wa shugabanni addu’o’i nagari zai sanya su iya aiwatar da kyawawan manufofin gwamnatocinsu ta yadda kasar nan za ta bunkasa a kowane fanni. Sai ya hori jama’ar Musulmi su ci gaba da yin aiki da darussan da suka koya a cikin watan Ramadan wajen tafiyar da rayuwarsu.
Sarkin ya tunatar da shugabanni su rika yin adalci da jagorancinsu bisa sanin ya kamata domin tsira daga hisabin da za a yi Ranar kiyama.
Ya yi wannan tunatarwa ne cikin hawaye yayin da ya kai ziyarar Barka da Sallah ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje a Hawan Nasarawa, inda ya ce mulki dai na Allah ne kuma Allah ne Yake ba da shi ga wanda Ya so, don haka akwai hisabi a kan masu mulki idan sun koma ga Allah.
Sarki Sanusi na II ya bukaci Gwamna Ganduje ya yi amfani da kwarewarsa wajen bullo da karin hanyoyin bunkasa Jihar Kano, musamman a fannin kula da lafiya da aikin gona da tsabtar muhalli da kuma ilimi.   
Daga Sakkwato, wakilinmu ya ce Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya lashi takobin sanya kafar wando da duk mahaifin da ya ki sanya dansa a makaranta, inda ya bukaci Majalisar Dokokin Jihar ta samar da dokar hukunta duk wanda aka samu da aikata hakan, don a bunkasa ilimi ga al’ummar jihar.
Gwamna Tambuwal ya fadi haka ne ga sarakuna da ’yan siyasar jihar lokacin da suka kai masa ziyarar Barka da Sallah a gidan gwamnatin a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce ya zama wajibi su samar da dokar idan aka yi la’akari da dimbin iyayen da suke kin sanya ’ya’yansu a makaranta da gangan.
Ya ce,  “Mun yi shiri na musamman da kwaliya za ta biya kudin sabulu inda za mu gina karin makarantu a matakin firamare da manyan asibitoci don kula da marasa lafiya 240 kuma za mu sanya musu duk wani abu da suke bukata. Za mu yi haka ne a dukkan yankunanmu uku da muke da su.”
Daga Katsina Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya ce gwamnatinsa ta yi nisa wajen kafa wani kwamiti na bayar da zakka, inda ya ce nan ba da jimawa ba zai mika wannan bukata ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewarta tare da maida shi doka. Gwamna Masari ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a ranar Hawan Bariki a tsohon gidan gwamnati, lokacin da Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya kai masa gaisuwa don bukukuwan karamar Sallar bana.
Gwamna Masari wanda ya tabo abubuwa iri-iri da gwamnatinsa ta riska daga gwamnatin da ta gabata, ya ce, baya ga bincike da gwamnatinsa za ta ci gaba da yi don kwato wa talakawan jihar dukiyoyinsu da wasu suka yi rub-da-ciki a kansu, har ila yau za a ba kowane mai hakki hakkinsa.
Sai ya ce zai yi iya kokarinsa don ganin cewa jihar ta samu ci gaba, ya ce gwamnatinsa da hadin gwiwa da gwamnatocin jihohin Kaduna da Sakkwato da Zamfara da Kebbi za su shawo kan matsalar barayin shanu da suka addabi yankin.
A jawabinsa ga al’ummar masarautar Katsina, Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir ya ja hankalin malamai su ci gaba da cusa da’a da tarbiyya a tsakanin al’umma musamman matasa, inda ya ce ba karamin hadari ba ne karancin tarbiyya a tsakanin matasa wanda hakan ne ke kai su ga shiga cikin matsaloli.
Sarkin ya yi kira ga jama’a su fito su karbi katin shaidar dan kasa wanda hakan zai bayar da dama hatta kan yadda za a yi rabon arzikin kasa. “Wannan kati zai kara kare mu daga hadduran da muke shiga, misali irin na Boko Haram wanda har yanzu an gaza gane ’yan kasa da bakin haure a cikinsu,” inji Sarkin.