✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka gano badakalar N400m a Gwamnatin Zulum

Ma'aikatu biyar sun yi gaban kansu wajen kashe Naira miliyan 400

Ofishin Babban Mai Binciken Kudade na Jihar Borno ya bankado yadda Naira miliyan 400 ta yi batan dabo a wasu ma’aikatu a Gwamnatin Babagana Zulum.

Rahoton Babban Mai Binciken Kudin Jihar Borno, Kashim Bukar, ya fallasa yadda wasu ma’aikatun Jihar guda biyar suka yi gaban kansu wajen kashe kudade a shekarar 2020.

Rahoton ya ce, “Hakika ba daidai ba ne a kashe Naira miliyan 400 ba tare da cikakkun bayanan yadda aka yi hakan ba.”

Ya ce duk da cewa Zulum ya kafa hukumar kula da sayayya ta gwamnati da kuma yadda yake bin diddigi wurin kashe kudade, akwai wasu jami’an gwamnati da ke masa zagon kasa, ba sa bin ka’ida ballantana cike takardun da suka dace kafin fitar da kudade.

Bullar rahoton yadda ma’aikatun suka yi gaban kansu wajen kashe kudaden ya bar baya da kura tare da sanya Zulum daukar wasu tsauraran matakai.

“Gwamna Zulum ya fusata kuma ya dauki tsauraran matakai a kai, amma ba ni da hurumin bayyana matakan da aka dauka,” a cewar Babban Mai Binciken Kudin. 

A ina aka yi?

An gano badakalar ta Naira miliyan 400 ce a Ma’aikatar Harkokin Addini da Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida da Ma’aikatar Aikin Gona da kuma Ma’aikatar Gidaje.

Aminiya ta nemi jin yadda hakan ta faru da kuma abin da gwamnatin Jihar ke yi kan abin da aka gano.

Zulum ta bakin kakakinsa, Isa Gusau, ya bayyana cewa,  “Gwamnatin Jihar Borno tana da girma kuma tana da cibiyoyin gwamnati da yawa ta yadda duk yadda Gwamna Zulum ya yi kokarin ganin an yi komai yadda ya kamata, ba za a rasa masu zagon kasa ba.”

A cewarsa, bayan kammala binciken kudaden na shekarar 2020, Bukar ya mika wa gwamnan rahoto mai shafi 153, shi kuma ya tura wa majalisar dokokin jihar tare da gabatar mata da kudurin doka da za ta yi wa tukfar hanci.

Wane matakin aka dauka?

Isa Gusau ya ce bayan bankado badakalar, Zulum ya umarci Ofishin Babban Mai Binciken Kudin Jihar Borno ya “Tsaurara bincikar hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar domin tabbatar da yin komai a fili.” 

Ya kuma umarce shi ya binciki yadda ma’aikatun jihar suka kashe kudaden gwamnati da nufin bankado cuwa-cuwa da kuma bayyana wa duniya ba tare da bin ta hannun gwamna ba.

Ya ce, “Tun kafin a wallafa rahoton, a watan Janairun 2020, Zulum ya kafa Hukumar Kula da Sayayya ta Gwamnati ya kuma dora mata alhakin tabbatar da yin komai babu kumbiya-kumbiya.

“Ba ya sa hannu kan duk wata takardar bukatar kashe kudi ba tare da an hado ta da bayanin yadda za a gudanar da kudaden ba, yana da tsauri a wannan bangaren.

“Ya kuma yaba wa Babban Mai Binciken Kudin bisa yadda ya fallasa ma’ikatun da ya samu da laifi, sannan ya ba shi kwarin gwiwar ci gaba domin sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnati su farka.”

Cuwa-cuwar ma’aikatu

Ya ce amma duk da tsaurin Gwamnan da wadannan matakan da ya dauka, wasu jami’an gwamnati na kokarin bi ta bayan fage.

“Ba sa bayar da bocar biyan albashi da sauran takardu tun daga 2016 lokacin da aka fara tantancewa ta hanyar zamani.

“A 2020 aka yi yunkurin bincikar kudaden albashi, inda aka samu wasu takardu, wanda hakan wata nasara ce.

“Yawancin bococin da aka yi ba a hada su da takardun shaidar da suke bukata ba.

“Hatta  takardun sahalewar yin sayayya ko rasidin saye ko sayarwa babu, wanda ke nuna cewa ko dai ba a sayi kayan ba, ko kuma ba su shigo hannu ba.

“Wasu takardun kuma babu sa hannun mutanen da suka dace a kansu, kamar masu sahalewa a yi sayayya ko kuma masu sayarwa.”

Sakacin masu bincike kudi?

Akwai kuma rashi ko karancin bin din diggigi a wurin tantancewa daga jami’ai masu binciken kudi na cikin gida a ma’aikatu, ba sa bin ka’idar aikinsu yadda ya kamata.

“Ba sa bin diddigi yadda ya dace wajen tabbatar da komai ya yi daidai kafin su buga hatimi a bisa takardu kamar yadda ka’idar aikinsu ta tanada.

“Amma duk da haka sun rage amfani da koren biro wanda doka ta takaita amfani da shi ga jami’an Ofishin Babban Mai Binciken Kudi na jihar.

“Rashin kwarewa da sakaci kuma sun zama ruwan dare a bangaren jami’an adana bayanan kudade.

“Ba sa hada bayanan kudade da takardun shaidar kashe kudaden da dalilin yin hakan yadda ya kamata.”

Me hakan ke nufi?

Rahoton da ya bankado badakalar ta Naira miliyan 400 ya ce, Gwamna Zulum ya cancanci yabo saboba shi ya sa a gudanar da binciken a kuma fitar da rahoton domin duniya ta gani.

“Sannan ya ba wa Babban Mai Binciken Kudi ’yancin cin gashin kai wurin gudanar da binciken, duk da cewa gwamnan ne na nada shi.

“Daga 2019 zuwa yanzu gwamnatinsa ta aiwatar da manyan ayyuka sama da 600 da suka ci biliyoyin Naira.

“Idan har Naira miliyan 400 aka gano ba a adana bayanan yadda aka kashe su yadda ya kamata ba, hakan na nufin rahoton ya samu an adana bayanan gomman biliyoyin Nairori yadda ya dace – Wannan abin a yaba ne.

“Tabbas ba daidai ba ne a kashe Naira miliyan 400 ba tare da cikakkun bayanan yadda aka yi hakan ba.

“Wannan ya fusata Gwamna kuma ya dauki tsauraran matakai a kai.

“Hasali ma, tun kafin fitar da rahoton gwamnan ya kafa hukumar kula da sayayya ta gwamnati domin tabbatar da ana yin komai a fili a bangaren sayayyat gwamnati.

%d bloggers like this: