✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka fara gasar Firimiyar Najeriya ta 2020/2021 da ba-zata

A ranar Lahadi, 27 da watan Disamba ne aka fara fafata gasar Firimiyar Najeriya ta kakar 2020/2021 inda aka fafata

A ranar Lahadi, 27 da watan Disamba ne aka fara fafata gasar Firimiyar Najeriya ta kakar 2020/2021 inda aka fafata wasanni shida.

Kakar ta bana dai ita ce kakar gasa ta 21.

Tun bayan dakatar da wasanni da aka yi a farkon shekarar nan saboda annobar Kwarona, sai a Lahadin ne aka dawo gasar a hukumance.

Kafin a dawo gasar, sai da kowace kungiya ta yi wa ’yan wasanta gwajin kwarona

Sauye-sauyen da aka yi a kakar bana

Daga cikin sauye-sauyen da aka kawo a kakar bana, akwai guda hudu da su ne muhimmai kamar haka:

  1. Kulob na iya kawo ’yan canji guda tara a wasa, inda za a iya amfani da canjin ’yan wasa guda biyar.
  2. Sannan ’yan benchi biyar ne kawai za su iya tashi atisaye a gefen fili a lokacin da ake buga wasa.
  3. Babu ’yan kallo a duk wasannin
  4. An kawo motocin daukan marasa lafiya

Yadda wasannin suka yi ba-zata

A shekaru da dama, babban abin da ke ci wa masu gasar Firimiyar Najeriya tuwo a kwarya shi ne yadda yake da wahala a zo har gida a lallasa kungiya, ko kuma karamin kulob ya lallasa babba.

Hakan dai ba ya rasa nasaba da yadda kowacce kungiya ce ke biyan alkalan wasa idan aka buga wasa a gidanta, da rashin wasu filayen wasa masu kyau da sauransu.

Tun a kakar bara aka fara samun sauyi a wannan bangaren, amma bana abin ban sha’awa, sai aka fara da ba-zata a wasannin.

A ranar farkon, mai rike da kambun gasar, wato Plateau United ce ta kwashi kashinta a hannu a gida, inda kungiyar Kwara United ta doke ta da ci biyu da nema a garin Jos.

Dan wasan Kwara United Jide Fatokun ne ya zura kwallo a ragar Plateau United a minti 62, sannan Michael Ohanu ya jefa ta biyun a minti na 69. Daga nan kuma aka yi ta tata-burza har aka tashi.

A wani wasan kuma, kungiyar FC Ifeanyi Ubah, wadda manyan ’yan wasanta suka barta saboda fama da take yi na rashin kudi, ta doke kungiyar da ta lashe gasar a kakar 2018, Lobi Stars.

Dan wasan Ifeanyi Ubah Nonso Nzediedwu ne ya zura kwallon a minti 47 da fara wasan.

Ifeanyi Ubah ta sha fama da rashin ’yan wasa masu kwarewa, inda a kakar bara aka doke kungiyar sau takwas a jere a gida da waje.

Wannan ya sa aka yi mamakin yadda ta doke kungiyar da ke daya daga cikin kungiyoyin da ake sa ran za su iya lashe gasar ta bana.

A garin Lafiya na jihar Nasarawa kuwa, kungiyar Wikki Tourist ce ta fara da jefa kwallo a ragar Nasarawa United a minti na biyar ta wajen Promise Damala.

Amma da aka dawo hutun rabin lokaci, kungiyar ta farke a minti bakwai, sannan ta kara na biyu a minti 52.

Dan wasan Nasarawa United Reuben Nicodemus ne ya zura kwallo biyu, inda ya zama dan wasan farko da ya zura kwallo biyu a kakar bana.

Haka ma, Kano Pillars da Adamawa United sun yi kunnen doki a gidan Adamawa United.

Kyaftin din Kano Pillars, Rabiu Ali ne ya zura kwallo a ragar Adamawa United a minti daya da fara wasa, kafin Isa Garba na Adamawa United ya farke a minti 75 da wasan.