Jihar Kano wadda ta yi kaurin suna wajen daukar fansa duk lokacin da rikici ya auku a Kudancin kasar nan, a wannan karo ta nuna dattako na rashin daukar fansar duk da harin da ’yan kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biyafara a karkashin Nnamndi Kanu ta kai wa ’yan Arewa mazauna Kudu a makon jiya. Wadansu ’yan kabilar Ibo sun far wa ’yan Arewa a Kudu maso Gabas suka kashe wadansu tare da raunata da dama, inda a Kano hukumomi da daidaikun mutane suka rika wayar wa al’ummar jihar kai kan su nisanci tayar da rikici ko daukar fansa.
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta bakin Kakakinta DSP Magaji Musa Majiya ta yi amfani da gidajen rediyo da talabijin wajen kiran jama’a su zauna lafiya tare da nisantar tayar da rikici a jihar, kiraye-lirayen da suka yi tasiri wajen tabbatar da zaman lafiya.
Al’ummar jihar a bangarensu sun bayar da hadin kai da bayar da goyon baya ga ’yan sanda don ganin an samu tabbataccen zaman lafiya a lokacin.
A ranar Asabar din makon jiya lokacin da ake rikici a Kudu maso Gabas, matasan Unguwar Fagge sun shirya fitar hawan dokin kara kamar yadda suka saba kowace bayan Sallah, amma saboda kusancin unguwarsu da Sabon Gari inda dimbin ’yan kabilar Ibo ke zaune sai ’yan sanda suka shawarci yaran da kada su gudanar da hawan don kauce wa abin da zai iya faruwa. Kuma wadannan matasa sun yi biyayya ga umarnin ’yan sandan.
Wani matashi da Aminiya ta zanta da shi, mai suna Saminu Tijjani ya ce, “Yanzu kan mutane ya waye, an fahimci idan aka yi rigimar a kan talakawa take karewa. Don haka al’ummar Jihar Kano sun daina tayar da rigima da sunan daukar fansa yayin da suka samu labari ana muzguna wa ’yan uwansu da ke Kudancn kasar nan. Idan a baya ne da tuni an dade da daukar fansa. Amma yanzu abin ba haka yake ba. abin da muke yi shi ne muna yin addu’a a samu tabbatacen zaman lafiya a ko’ina a fadin kasar nan.”
Haka ’yan boko sun bayar da gudummawa wajen hana tashin rikici a jihar, inda suka yi ta amfani da shafukan sada zumunta suna watsa sakonnin kwantar da hankali da yin kira ga jama’a su guji daukar fansa a kan abin da ke faruwa a Jihar Abiya da wasu sassan garuruwan Ibo. Har ila yau ’yan bokon sun yi kokari wajen karyata hotuna da labaran karya da ake watsawa a shafukan sadarwa game da abin da ke faruwa a Kudu da nufin tunzura jama’a su dauki fansa a kan ’yan kabilar Ibo da ke jihar.
Binciken Aminiya ya gano cewa ’yan kabilar Ibo mazauna Jihar Kano suna cikin kwanciyar hankali tare da gudanr da harkokinsu na kasuwanci kamar yadda suka saba.
Aminiya ta gano cewa a Kasuwar Saban Gari da wasu wurare da ’yan kabilar Ibo suke gudanar da harkokinsu koma na tafiya sumui-lumui babu wata alama ta zaman dar-dar ta yiyuwar barkewar rikici.
Kuma Aminiya ba ta samu labarin yin kaura daga bangaren ’yan kabilar Ibo ba, kuma babu wadansu mutane da suka karu a tashohin mota da ke jigila zuwa Kudu, kamar yadda jami’an babbar tashar da ke New Road a Sabon Gari suka tabbatar mata cewa ba a samu masu yin kaura daga Kano zuwa Kudu, kamar yada aka saba a baya ba.