’Yan sanda sun ceto wasu mutum 113 da ke tsare a wata haramtaciyyar makarantar gyaran hali, inda ake azabtar da su, har hakan ya yi sanadin mutuwar daya daga cikinsu a garin Kano.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke mutum shida da ke gudanar da haramtaccen gidan marin da aka bankado a unguwar Na’ibawa ’Yan Lemo a Karamar Hukumar Kumbotso.
- Daga Laraba: Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a cikin al’umma
- Ranar Hijabi: Kalubalen da mata masu hijabi suke fuskanta
“A ranar 1 ga watan Janairu mun samu rahoton cewa mutum 10 daga cikin wadanda aka tsare a wani gidan mari da ke Na’ibawa ’Yan Lemo a Karamar Hukumar Kumbotso sun tsere.
“Sun kuma sanar da mu cewa daya daga cikin wadanda aka tsare mai suna Aminu Ado mai shekara 22 ya rasu sakamakon azabtarwa,” a cewarsa.
Kiyawa, ya ce bayan samun rahoton Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Samaila Shuaibu Dikko, ya umarci tawaga ta musamman karkashin jagorancin CSP Abdulkarim Abdullahi don ceto wadanda aka tsare a makarantar.
“Bayan isa gidan muka tabbatar da rahoton abin da aka aike mana, mun ceto mutum 113 dauke da raunkuna daban-daban, wadanda kuma aka tsare su tsawon lokaci kuma tuni an mika su Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed don duba lafiyarsu, kafin a mika su ga Gwamnatin Jihar Kano.
“Sannan mun cafke mutum shida da ake zargin su ne suke kula tare da tafiyar da gidan marin da ke unguwar Na’ibawa ’Yan Lemo.”
Kakakin ya ce wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa sun shekara 10 suna gudanar da makarantar duk kuwa da dokar haramci da gwamnatin jihar ta kafa kan ire-iren wadannan makarantun na gyaran halin.
Kiyawa ya kara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da mika wadanda ake zargin a gaban kotu don yanke musu hukuncin da ya dace.