Wasu leburori da kamfanin da suke wa aiki ya kulle ya kuma tilasata musu yin aiki na kusan wata uku ba tare da zuwa gida ba sun samu kubuta bayan ‘yan sanda sun kai samame a wurin.
Wani daga cikin ma’aikatan da aka kubutar mai suna Sani Kiru ya ce wadanda aka kubutar sun kai mutum 300 a kamfanin na wasu ‘yan kasar Indiya.
Amma Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Habu Sani Ahmadu ya ce leburori 126 ne suka kubutar a kamfanin shinkafar ‘Popular Farm’ sabanin rahotannin da ke cewa sun kai 300 zuwa 600.
“Kusan wata uku an mayar da su kamar bayi”, inji kwaminshin ‘yan sandan.
“Ranar Litinin aka kubutar da dukkanninmu. Abin ba dadi, ban san yadda zan kwatanta irin abincin da aka rika ba mu ba”, inji Sani Kiru.
- Ba mu da shirin sake bude makarantu yanzu – Gwamnatin Kano
- Kano ta bude shafin COVID-19 a intanet
- Coronavirus: Ma’aikatan lafiya 29 sun kamu, an rufe asibiti a Filato
Ya shaida wa wakilinmu cewa shugaban gudanarwan kamfanin ya dauko wata mata da ta zo tana sayar musu da abinci a wurin.
“Albashina N32,000 ne a wata. Muna aiki ba dare ba rana. Ina son zuwa gida amma ba hali; matata da ‘ya’yana sun shiga damuwa”, inji shi.
—Yadda aka kulle leburori a cikin masana’antar
Wakilinmu ya jiyo cewa Indiyawan masu kamfanin da ke yankin Challawa a jihar Kano, sun ce sun rufe ma’aikatan ne domin dakile yaduwar cutar coronavirus.
Shaidu sun ce ma’aikatan sun dade suna aiki da kamfanin, amma da cutar coronavirus ta bulla sai Indiyawan suka kulle su a ciki suka hana su tafiya gida.
—An goga musu zuma a baki, an yaudare su
Majiyarmu ta ce sakamakon haka masu kamfanin sun yi wa ma’aikatan karin albashi, amma kuma suka yi barazanar korar duk leburan da ya yi yunkurin fita daga harabar kamfanin.
“Masu masana’antar sun kulle su ne jim kadan bayan Gwamnatin Jihar Kano ta rufe iyakokinta ta kuma hana shiga ko fita daga jihar a ranar 27 ga watan Maris, 2020, inji majiyar.
“Indiyawan sun yaudari ma’aikatan cewa za su zauna a masana’antar ne na dan lokaci.
Ta kara cewa, “maimakon su bar ma’aikatan su rika zuwa wurin iyalansu, sai suka yi barazanar korar duk wanda ya ce zai bar wurin kuma ba za su kara daukar sa aiki ba”.
— Yadda ‘yan sanda suka kai samame
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ce rundunar ta kai samame a masana’atar da ta kubutar da mutum 126 din ne bayan ta samu izinin kotu kan takardar koken da kungiyar Global Human Rights Network, mai rajin kare hakkin dan Adam ta rubuta.
Majiyoyi sun ce ‘yan sanda sun yi awon gaba da manajojin kamfanin guda hudu, ko da yake kwamishinan ‘yan sandan bai ce akwai wadanda suka kama ba.
“Muna bincike…za mu sanar da ku idan akwai wani abu, amma babban abun shi ne an kubutar da mutanen da kamfanin ya tsare”.
Kakakin rundunar ya ce ana binciken masu kamfanin bisa zargin “tilasta wa mutanen zama ba da son ransu ba”.
— Suna aiki ba dare ba rana a kullen
Yawancin ma’aikatan da aka zanta da su sun koka cewa suna aiki a tsawon lokacin ne ba tare da samun isasshen abinci ba.
“Dan takaitaccen lokaci kawai ake bari mu huta, ba zuwa gida,” inji wani dan28 daga cikin leburorin.
Shi ma wani daga cikin ma’aikatan ya ce tun ranar 23 ga watan Maris yake kulle a kamfanin ba tare da ko da fita waje ba.
Wani wanda ya ce tun ranar 28 ga Maris yake aiki ya ce, ko iyalansu sun zo kamfanin ba ya bari su je su gan su.
“‘Yan uwanmu da iyalai sun damu…ba su san halin da muke ciki ba. Matata da ‘ya’yana sukan zo kofar masana’antar amma ba ni da damar zuwa in gan su”.
— Yadda ma’aikatan suke rayuwa a kulle
“Abin da na gani na da matukar tayar da hankali domin wurin da aka ajiye su ko dabbobi sai haka”, inji Kabiru Yahaya Kabara na Global Human Rights Network.
Ya ci gaba da cewa,”Abincin da ake ba su ba ya kosarwa, sannan babu magani domin wadanda ba suka kamu da rashin lafiya”.
Hotunan wurin da aka yada sun nuna cewa leburorin na cushe ne a wani dakin kwano da aka yi na wucin-gadi. Babu gadaje, sai tabarmi da leburorin ke kwanciya a kai.