Mamba a kwamitin, Dokta Atta, ya zargi manyan masu shiga tsakani, ciki har da fitaccen dan jarida, Tukur Mamu, da yin duk abin da za su iya na hana gwamnati ceto mutanen saboda neman biyan bukantun kansu.
- An gano gawa 13, mutum 10 sun bace a hatsarin kwalekwale a Zamfara
- NAJERIYA A YAU: Yadda Abinci Ke Kashe ’Yan Najeriya
- Abin da kasafin Buhari na karshe zai kunsa
A cewar Atta wanda mahaifinsa ke cikin fasinjoijn da aka yi garkwua da su, da farko masu garkuwar ba su nemi kudi ba, Tukur Mamu ne ya shigar da maganar kudi, wanda ya kara dagula lamarin.
Ya ce, “Shigar da batun biyan kudi da Mamu ya yi ya sa iyalan mutanen da sace biyan sama da Dala 200,000, kafin Babban Hafsan Tsaron Najeriya ya shiga lamarin.”
Ya yi wannan zargi ne a lokacin da ake bayani kan yadda aka ceto mutanen, a hirar da aka yi da shi kai-tsaye a tashar talabijin na Channels.
Yadda aka ceto fasinojin jirign kasa
A cewarsa, “’Yan Kwamitin Shugaban Kasa sun sayar da ransu, saboda sai da muka shiga cikin dajin muka yi magana da ’yan ta’addan, har kwana mun yi a cikin dajin.”
“Muna kuma godiya ga Gwamnatin Tarayya da Babban Hafsan Tsaron Najeriya bisa taimakon da suka yi mana, har muka iya shiga cikin daji muka dawo da ’yan uwanmu da suka rage a hannun masu garkuwa da su.
“Wannan nasara da aka samu babu hannun wani mai cin amanar kwamitin da gwamnati, ina nufin Tukur Mamu, wanda ya yi duk abin da zai iya domin kawo cikas ga yunkurin gwamnati domin neman biyan bukatar kansa.
“Sanin kowa ne cewa yanzu yana tsare a hannun gwamanti, amma muna godiya ga Allah, ’yan uwanmu sun dawo baki dayansu.
“Mun gode Allah Babban Hafsan saron Najeria da a shiga lamarin a kafa kwamiin da bai nemi ko kobo ba.
“Ina tabbatar muku cewa a cikin kwamitin na yi aiki da mutane masu matukar nagarta da rikon amana.
“Da ina da hali da kowannensu sai an ba shi lambar girmamawa ta kasa saboda yadda suka sadaukar da rayukansu, suka shiga daji suka kwana.
“Abin da ya kamata a yi nan gaba, shi ne hukumomin tsaro su rika hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu sannan gwamnati ta kara bayar da damar ci gaba da tattaunawa.”