’Yan sanda sun cafke wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi Jihar Zamfara, suka kuma ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a yankin Gada da ke Karamar Hukumar Bungudu ta jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ayuba Elkanah, ya ce hadin gwiwar ’yan sanda, sojoji da ’yan banga ne suka kai samamen, inda suka yi dauki ba dadi da ’yan bindigar har suka yi nasarar ceto mutum 10, ciki har da wata karamar yarinya mai shekara daya a duniya.
- Yadda gobara ta lakume kasuwanni 2 a Sakkwato
- Najeriya A Yau: Tattalin Arziki: Yadda 2021 Ta Zo Wa ’Yan Najeriya
“Jami’an tsaron sun yi gumurzu kafin daga bisani aka ceto mutanen sannan aka kama kasurgumin dan bindigar daji mai suna Sani Mati, wanda ake wa lakabi da Mai-’Yanmata,” inji Kwamishinan ’Yan Sandan.
Ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa an cafke Mai-’Yanmata ne a yayin da yake kokarin tare hanya don satar mutane a hanyar kauyen Koliya.
Elkanah, ya ce a baya Mai-’Yanmata yana tare da kasurgumin dan bindigar jihar, Bello Turji ne, amma yanzu ya koma karkashin Kachalla Sani da ke ayyukansa a yankunan Zurmi, Shinkafi da Birnin Magaji.
“An cakfe shi dauke da bindiga kirar AK-47, harsasai da babur kirar Boxer, yanzu haka yana hannu ana bincike a kansa kafin mika shi zuwa kotu don yanke masa hukunci.
“Yanzu haka komai ya koma daidai a yankin da abun ya faru, kuma za a ci gaba da kara kaimi wajen kawo karshen ayyukansu,” inji Elkanah.