✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda a ke magance kumburin idanu

Kumburin idanu na faruwa ne sakamakon yawan kuka ko yawan amfani da idon wajen karatu ko aiki a kan na’urar kamfuta. Wasu kuma kumburin idanunsu…

Kumburin idanu na faruwa ne sakamakon yawan kuka ko yawan amfani da idon wajen karatu ko aiki a kan na’urar kamfuta. Wasu kuma kumburin idanunsu na da alaka da wani canji da aka samu a gangar jiki ko don yanayi walau kura ko rana. Wasu kuma nasu na faruwa ne saboda rashin bacci ko kuma cin  abincin da ba ya dauke da sinadaran gyaran ido.
Ido na daya daga cikin abubuwan da ake fara gani a fuska don haka ya kamata mu kula da idanuwanmu. Akwai hanyoyi da dama da yakamata abi don magance wadannan matsalolin kumburin ido kamar haka;
•Shan ruwa- hanya ce mafi sauki wajen magance kumburin ido domin, ruwa na wanke wasu datti a ido. Yawan shan ruwa  yana da kyau, a sha ruwa a kalla kofi takwas zuwa goma a rana. Sannan kuma yana da kyau a rage cin gishiri.
• A samu cokular karfe kamar biyar zuwa shida a saka a firiji na tsawon mintuna  goma zuwa goma sha biyar sannan a ciresu, sai a dinga shafawa a kumburin ido har sai ido ya sabe.
•Ganyan shayi na magance kumburin ido; a jika ganyen shayi a ruwan dumi, sannan a cire a bari ya huce. A kwanta a daura jikakkiyar jakar ganyen shayin a kan idanu sai a rufe idanu da kyalle mai tsafta. A bari ya tsaya a hakan na tsawon mintuna biyar zuwa goma sannan a cire.
•Wata hanyar magance kumburin ido it ace; a sami gurji sai a yanka sannan a saka a firiji na tsawon mintuna goma sai a cire a daura akan idanuwan har sai sun huce.