✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ƙona Alƙur’ani ya yamutsa Sweden

Ƙona Alƙur’ani mai girma ya jefa ƙasar Sweden cikin ruɗani game da ƴancin faɗin albarkacin baki da kuma kare haƙƙin addinin marasa rinjaye. Karon battar…

Ƙona Alƙur’ani mai girma ya jefa ƙasar Sweden cikin ruɗani game da ƴancin faɗin albarkacin baki da kuma kare haƙƙin addinin marasa rinjaye.

Karon battar dake tsakanin manufofin biyu ta kuma jawo tarnaƙi ga yunƙurin Sweden na shiga ƙungiyar ƙawancen tsaro ta ƙasasashen arewacin Tekun Atalantika (NATO).

Sweden dai ta matsu da ta shiga NATO sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine amma bisa ƙa’ida ƙungiyar ba ta karɓar wata sabuwar ƙasa sai duk ƙasashen dake cikinta sun amince.

Ba da yawunmu aka kona Alkur’ani ba, muna Allah wadai – Gwamnatin Sweden

Sweden ta amince a ƙona Alƙur’ani ranar Sallah

Daga cikin ƙasashen dake NATO kuma akwai Turkey wacce ta ƙi amincewa da shigar Sweden saboda zanga-zangar adawa da Musulunci da ake gudanarwa a ƙasar.

Ƙona Alƙur’ani ranar Sallah

A makon jiya ne dai  wani Kirista ɗan asalin Iraq ya ƙona littafin Alƙur’ani mai girma a ƙofar wani masallaci dake Stockholm, babban birnin Sweden a ranar Sallah Babba.

Kuma ya ce ya aikata hakan ne domin nuna tsananin ƙiyayyar da yake yi wa littafin.

Ƙonawar ta jawo Allah wadai daga ƙasashen Musulmi, kuma ta jawo muhawara a ƙasar Sweden game da iyakar ƴancin faɗin albarkacin baki.

A yanzu kuma sai ga labari daga ƴan sandan Sweden cewa sun sake samun takardun neman izini daga wasu mutanen da ke son sake ƙona Alƙur’ani tare da Attaura da Baibul.

Kasashen Musulmi sun nemi Sweden ta haramta waɗanann ayyukan na tsokana da cin zarafin addini yayin da Firaministan Pakistan Shehbaza Sharif ya yi kira da a fito zanga-zangar kare martabar Alƙur’ani a ranar Juma’a, lokacin da majalisar dokokin ƙasar za ta tattauna game da ƙona Alƙur’anin da aka yi a Sweden.

Sweden ta Rikice

Hatta wasu daga cikin masu rajin kare haƙƙin faɗin albarkacin baki a Sweden sun ce irin wanann zanga-zangar daidai take da kalaman ƙiyayya, wanda haramun ne a ƙasar matuƙar ya shafi wata ƙabila ko jinsi.

Amma wasu da dama a Sweden na ganin dole ne a bada damar cigaba da  sukan addini, ko da kuwa ta hanyar da za ta baƙantawa mabiyansa ne kuma wajibi ne ƙasar ta kiyayi dawo da dokokin da suka haramta keta alfarmar addinai waɗanda tun tuni aka soke su a ƙasar.

Shirin gasar fitar da zakarun jima’i a Sweden ya tarwatse

Kona Alkur’ani a Sweden ya jawo Allah-wadai daga kasashen Musulmai 

A cewar wani mai fashin baƙi kan harkokin tsaro a ƙasar, Magnus Ranstorp “Sweden na cikin tsaka mai wuya”.

A ranar Larabar nan ne shugaban Amurka Joe Biden ya karɓi baƙuncin Firaministan Sweden Ulf Kristersson a fadar White House inda ya jaddada muhimmancin shigar Sweden cikin ƙungiyar NATO.

A cewarsa shigar Sweden zai ƙara ƙarfafa ƙawancen NATO.

Za a Ƙona Baibul

A Larabar ne kuma ƴan sandan Sweden suka ce sun karɓi takardu biyu na neman izinin ƙona littatafan addini a birnin Stockholm: ɗaya daga wani da yake son ƙona Alƙur’ani a ƙofar masallaci yayin da ɗayan ke son ƙona Attaura da Baibul a ƙofar Ofishin Jakadancin Isra’ila.

Roƙo na uku kuma ya fito ne daga wani mutumin a birnin Helsingborg dake kudancin ƙasar wanda ya nemi izinin “ƙona littafin addini”.

Kawo yanzu dai ƴan sanda ba su yanke hukunci kan roƙon ba.

An kama masu zanga-zanga kan yunkurin kone Alkur’ani a Sweden

Mace ta farko da aka zaba Firaminista a Sweden ta yi murabus sa’o’i bayan nada ta

Shugaban ƴan sanda na yankin Helsingborg ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa “a Sweden, muna da ƴancin faɗin albarkacin baki. Muna kuma girmama mutanen dake da ra’ayi mabambanci, sannan ba ma son abin da zai ɓata musu rai. Don haka lamarin na buƙatar nazari.”

A farkon shekarar nan dai ƴan sandan Stockholm sun yi ƙoƙarin hana ƙona Alƙur’anin amma kotu ta ce dokokin Sweden sun amince da yin hakan.

Bisa la’akari da wannan hukuncin ne, ƴan sanda su ka bada dama a makon jiya wani Kirista ɗan Iraq ya ƙona Alƙur’ani mai girma a ƙofar masallaci ranar Sallah Babba.

Musulmi sun Koka

Jagororin Musulmi a Sweden sun yi tur da wannan aiki amma martani mafi zafi ya fito ne daga ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Masu zanga-zanga sun afkawa Ofiishin Jakadancin Sweden dake Baghdad. Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) ta soki hukumomin Sweden da suka bari aka yi.

Iran ta dakatar da tura sabon jakada zuwa Stockholm yayin da Pakistan ta buƙaci Majalisar Kare Haƙƙin Bil Adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya zama na musamman akan batun.

Ba Musulmi kaɗai ba, hatta Fafaroma Francis ya koka da lamarin.

Gwamnatin Sweden ta yi Suka

A nata ɓangaren, gwamnatin Sweden ta ce ta na “tsananin adawa da ayyukan nuna ƙiyayya ga Musulunci da wasu mutane ke aikatawa a Sweden” kuma ta ce “hakan bai dace da ra’ayin Gwamnatin Sweden ba.”

Hakan ya jawo ƴan gwagwarmaya a ƙasar suka yi ta sukan gwamnati inda suka tuhume da rashin kare haƙƙin faɗin albarkacin baki.

Fitaccen mai rajin kare haƙƙin faɗin albarkacin baki a Sweden Nils Funcke ya  shaidawa gidan talabijin na gwamnatin ƙasar, SVT cewa, “ba daidai ba ne ko kaɗan a cewa gwamnati na sukar wani mutum da ya aikata abinda bai saɓawa doka ba, illa dai kawai ya yi amfani da haƙƙin da tsarin mulki ya tabbatar masa na faɗin albarkacin bakinsa.

Makomar Denmark

Sweden dai ta na fargabar kar ta tsinci kanta a irin halin da Denmark ta shiga a 2006 bayan da wata mujalla ta wallafa hotunan cin zarafa da ta danganta su da Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

A lokacin an ƙona ofisoshin jakadancin Denmark yayin da masu zanen suka fuskanci barazanar kisa daga masu kishin Musulunci.

Duk ƙoƙarin da jami’an Denmark suka yi a lokacin na bayyana cewa haƙƙin faɗin albarkacin baki ya dace da doka basu gamsar da ƙasashen Musulmi ba.

A binciki Rasha

Sai dai Hukumar Tsaro ta Sweden na zargin da hannun Rasha cikin wanann shiri na ƙona Alƙur’ani a makon da jami’an ƙasar za su tattauna da takwarorinsu na Turkey game da buƙatar shiga ƙawancen NATO.

Kakakin hukumar Adam Samara ya ce “Hukumar Tsaron Sweden na sane da yadda ƙasashe irin su Rasha ke juya  akalar wasu mutane daga bayan fage domin kawo ruɗani a ƙasar Sweden.”

Ƙasashen Sweden da Finland, waɗanda a da ƴan-ba-ruwana ne sun nemi shiga NATO ne bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a bara.

Kuma Rasha ta gargaɗe su da cewa za ta mayar da martani da “matakan siyasa da na soji.”

A watan Afrilu Finland ta shiga NATO, amma Turkey da Hungary sun ƙi amincewa da shigar Sweden.