Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi shi ne asibiti mafi girma a Jihar Bauchi bayan mika shi ga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa a shekarar 2010 inda aka daga darajarsa daga babban asibiti zuwa Asibitin Koyarwar.
Sai dai duk da ingancin asibitin, akan samu koke-koke daga marasa lafiya da ke zuwa don ganin likita, kama daga masu korafin tsada zuwa masu nuna rashin gamsuwa da yadda ake kula su a asibitin, yayin da wasu suke hamdala da asibitin.
- Ba mu sanar da ranar da jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki ba – NRC
- An sace Mataimakin Daraktan IAR da ke Zariya
A baya-bayan nan wani jami’in tsaro mai suna Usman Mu’azu ya nuna rashin gamsuwarsa inda ya zargi likitocin asibitin da yin sakaci kan jinyar dansa da ya samu karaya a hannu, inda ya yi zargin cewa likitocin asibitin sun yi masa kora da hali.
Sai bayan wata 3 za mu samu ganin likita
Da yake zantawa da wakilin Aminiya a Bauchi, Usman Mu’azu, ya ce, “Dana mai suna Muslim Usman mai shekara hudu zuwa biyar, ya karye kusan mako uku, an yi daurin gida ba a dace ba, na tafi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda suka ce min idan ina so a gyara sai dai in tafi wani asibitin mai zaman kansa da suka yi min kwatance da ke aiki a farashi mai tsada da ba ni da halin biya a lokacin, ko (in ina so a ATBUTH), in jira sai ranar 11 ga watan Janairu, 2023.
“Na ga ba zan iya barin yaron da ciwo har zuwa wannan lokaci ba, sai na sake komawa ga gargajiya tare da hoton kashin, suka duba suka sake karyawa suka yi sabon dori da fatar Allah Ya sa a yi a sa’a,” in ji shi.
Mahaifin ya kara da cewa, “Da farko mun fara zuwa Asibitin Kwararru na Jihar Bauchi ne, ba mu samu ganin likita ba, sai muka dawo Asibitin Koyarwar.”
Kuma ya ce, dan nasa ya samu karaya ne lokacin da yake dawowa daga makarantar Islamiya a ranar 28 ga Satumban bana.
Ya ce, “Da farko an za ci targade ne. Da na lura abin bai yi sauki ba bayan dorin, sai muka kai shi Asibitin Koyarwa muka yi hoton kashi aka gano karaya ce.
“Sai muka yi kokarin a yi mana aiki, su kuma suka ce mana mu bari sai ranar 11 ga watan Janairu, 2023, kimanin wata uku nan gaba, kafin mu ga likita.
“Abin mamaki, da na zo asibitin sai aka ce mu je a dauki hoton hannun a gani, amma bayan an dauki hoton sakamakon ya fito, sai aka ce in jira sai 11 ga Janairun badi kafin likita ya yi aiki a hannun. Sai na ga wannan daidai yake da kora da hali.”
Dole na sauya dabara —Mahaifin mara lafiya
Mahaifin ya ce, “Bayan an yi hoto sai aka tura mu wajen da ake ajiye masu hadari, a nan ne muka samu wannan matsalar inda ma’aikatan jinya suka ce wai mu koma gida sai ranar 11 ga watan Janairun 2023 in dawo da yaron.”
Ya ce, “Ganin hakan ya yi nisa ne na nemi wata hanya ta sama wa dana lafiya, na kai shi wani wuri aka yi masa gyara, yanzu yana nan yana samun sauki cikin ikon Allah.”
Mu’azu ya ce, “Lokacin da na kai shi ba su nuna bacin rai saboda na kai shi wajen gargajiya kafin daga bisani na kawo shi wajensu ba.
“Na ce idan dansa ne zai jira tsawon lokacin nan kafin a yi masa aiki?
“Suka dauko mini wata doguwar takarda, suka ce ai ba laifinsu ba ne, suka nuna min jerin sunayen mutanen da suke gabana, wadanda duk sun nemi mafita domin ba wanda zai tsaya jiran wadannan ranakun da suka bayar.
“Akwai wani daga cikinsu nas din da ya ba ni shawara in je wani asibiti ta wajen makarantar Dolphin na kashi don a yi mana aikin cikin gaggawa, amma ban saurare shi ba,” in ji shi.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Babban Likitan Asibitin ABTUTH, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.