✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya yi wa karamar yarinya fyade ya kashe ta

Wani matashi da ya yi wa wata yarinya fyade ta mutu ya shiga hannu a Jihar Nasarawa.

Wani matashi da ya yi wa wata yarinya fyade tare da kashe ta ya shiga hannu a Jihar Nasarawa.

’Yan sanda a jihar sun cafke matashin mai shekara 36 ne bayan ya tursasa wa budurwar mai shekara 17 ta sha maganin kashe ciyawa na gramoxone, sannan ya yi lalata da ita a Karamar Hukumar Nasarawa-Eggon ta jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce jami’ansu sun bi sawun wanda ake zargin kuma sun yi nasarar kama shi.

Ya ce, “Wani magidanci mai ya kai kara babban ofishin ’yan sanda da ke Akwanga cewa wani mai suna Bako Anjeh ya yaudari ’yarsa zuwa dakinsa domin yin lalata da ita.

“Da ta ki amincewa sai ya tursasa ta sha wani maganin kashe ciyawa mai suna gramoxone, wanda bayan ta sha shi ta galabaita, shi kuma ya yi mata fyade.

“Bayan samun rahoton ne muka jami’anmu zuwa wurin kuma suka yi nasara kama wanda ake zargin.

“An kai yarinyar Asibitin Ola da ke Karamar Hukumar Akwanga inda a nan ta yi bayani, daga bisani rai ya yi halinsa, aka ajiye gawarta domin gudanar da bincike.