✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi wa diyarsa ’yar shekara 14 ciki a Delta

Rundunar ’yan sandan Jihar Delta ta bayyana  cewa tana neman Lucky Akuna, mahaifin wata yarinya da ake zargi ya yi mata ciki ya gudu. Lamarin…

Rundunar ’yan sandan Jihar Delta ta bayyana  cewa tana neman Lucky Akuna, mahaifin wata yarinya da ake zargi ya yi mata ciki ya gudu. Lamarin dai ya faru ne a wani kauye da ke karamar Hukumar Ugboroke Ubwie.

Bayanai da suka fito daga rundunar ’yan sandan jihar sun nuna cewa yarinyar ce da kanta ta je ta sanar wa ofishin nasu, cewa mahaifinta da wani dan uwanta ne suke kwana da ita, suke rika yin musayar kwana tsakanisu da ita, wanda sanadiyyar haka kuma ta samu juna biyu.

A kokarin da ’yan sanda suka yi na kama mahaifin yarinyar tare da dan uwan nata, ya sanya suka tsere daga gidansu. Yarinyar da aka sakaya sunanta, ’yar shekara 14 da haihuwa, ta yi wa ’yan sanda bayanin cewa yayanta da mahaifinta ne suka rika raba kwana da ita.

Bayanai da Aminiya ta samu daga wata majiya, sun nuna cewa makwabtansu ne suka ga alamun cikin ya girma, su kuma suka sanar wa jami’an tsaro. Wani daga cikin makwabtan mutumin da ake zargi, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: “Wannan ba shi ne na farko ba, ko a kwanan baya ma mutumin ya yi wa wasu ’ya’yan yayyensa uku ciki a lokuta daban-daban.” Ya kara tabbatar wa manema labarai cewa yarinyar suka kirawo, suka matsa mata lamba da tambaya, ya aka yi ga ta karamar yarinya ’yar shekara 14 da haihuwa ta samu ciki, waye ya yi mata? Shi ne ta ce ai babanta ne da kuma yayanta suka rika musayar kwana da ita har ma ta samu cikin.” 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Delta, Andrew Aniamaka yace rundunarsu ta sha alwashin kama mahaifin yarinyar da ya gudu, wanda ake zargin ya bata rayuwar ’yar tasa.