✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi wa dalibarsa fyade a aji tana tsaka da rubuta jarrabawar WAEC

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Ogun ta cafke wani malamin makaranta mai kimanin shekaru 26 Mathew Adebayo bisa zargin yiwa wata dalibarsa mai kimanin shekaru 15…

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Ogun ta cafke wani malamin makaranta mai kimanin shekaru 26 Mathew Adebayo bisa zargin yiwa wata dalibarsa mai kimanin shekaru 15 fyade.

An cafke Mathew wanda malami ne a wata makaranta mai zaman kanta bayan da shugabar makarantar ta kai kararsa wajen ‘yan sanda.

Kakakin rundunar a jihar Abimbola Oyeyemi shine ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a birnin Abeokuta ranar Juma’a.

Ya kuma ce sun yi wa wanda ake zargin dirar mikiya ne bayan da daya daga cikin daliban aji ukun babbar sakandire ta tabbatarwa da shugabar makarantar cewa Mathew ya sha yi wa yarinyar fyade tun lokacin da aka sake bude makarantu a jihar a shirye-shiryen fara rubuta jarrabawar WAEC.

Ya ce malamin ya rika yi mata barazanar cewa ba za ta ci jarrabawar ba muddin ta ki ba shi hadin kai.

Hakan ne kuma ya ba shi damar jan yarinyar zuwa cikin wani aji ya kuma ci gaba da lalata da ita.

“Amma da tura ta kai bango ta ga ba za ta iya ci gaba da jurewa ba sai ta yanke shawarar kai kararsa wurin shugabar makarantar,” inji kakakin.

Abimbola ya ce da samun rahoton ne sai babban baturen ‘yan sandan yankin Sango, CSP Godwin Idehai ya baza komar jami’ansa wadanda kuma su ka sami nasarar cafko malamin.

Ya ce tuni wanda ake zargin ya amsa aikata laifin yayin da ita kuma yarinyar ke asibiti tana ci gaba da samun kulawa.

Kakakin ya kuma ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Edward A. Ajogun ya umarci a mayar da wanda ake zargin zuwa bangaren yaki da fatauci da bautar da kananan yara na sashen masu aikata manyan lafuffukan rundunar domin fadada bincike.