✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi garkuwa da ’yar cikinsa yana neman kudin fansa daga matarsa

Ya bukaci matarsa ta biya kudin fansa Naira miliyan biyu in ba haka ba zai kashe yarinyar

An gurfanar da wani magidanci a gaban wata Kotun Majistare da ke Sansanin Alhazai a Jihar Kano bisa zargin yin garkuwa da ’yar cikinsa tare da neman kudin fansa daga matarsa wacce ita ce kuma mahaifiyar yarinyar.

Mutumin dai na neman Naira miliyan biyu daga wurin matar domin sakin yarinyar kafin daga bisani dubunsa ta cika.

’Yan sanda sun shaida wa kotun cewa matar mutumin ta yi zargin cewa an yi garkuwa da yarinyar mai kimanin shekara hudu da haihuwa.

A cewar matar, mijin nata ya yi barazanar kashe yarinyar matukar ba ta biya kudin fansar ba.

Binciken ’yan sanda ya gano cewa bayan mako biyu, mahaifin yarinyar ya rika kiranta a waya don ta biya kudin fansa, kafin daga karshe a samu yarinyar a wurinsa.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Sakina Aminu ta yi umarnin da a tsare wanda ake zargin a gidan yari tare da sanya ranar 24 ga watan Nuwamba don ci gaba da sauraren shari’ar.