✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya yi garkuwa da ma’aikatan banki kan hana shi cire kudinsa

Bassam mai shekara 42 ya bukaci bankin ya ba shi Dala 2,000 daga asusun ajiyarsa ya biya wa mahaifinsa kudin asibiti amma bankin ya hana…

Wani mutum ya yi garkuwa a ma’aikatan bankin da yake ajiya tare barazanar kashe su sannan ya kona kansa idan bankin bai ba shi kudin ajiyarsa ya biya wa mahaifinsa magani a asibiti ba.

Mutumin mai suna Bassam Sheikh Hussein ya yi garkuwa ne da mutum takwas — jami’an banki shida da kwastomomi biyu — a bankin Banque du Liban a birnin Beirut na kasar Lebanon, bayan an dakatar da asusun ajiyarsa tun a shekarar 2019.

Da farko Bassam mai shekara 42 ya bukaci bankin ya ba shi Dala 2,000 daga asusun ajiyarsa domin ya biya wa mahaifinsa kudin asibiti amma bankin ya hana shi.

Daga nan ne ya zaro bindiga, ya umarci kwastamomin da ke cikin bankin su fice, kana ya tsare mutum takwas din, sannan ya zuba fetur a jikinsa da harabar bankin.

Daga nan ya yi  barazanar kashe muta nen tare kona kansa da bankin, muddin ba su ba shi Dala 2,000 da zai biya wa mahaifinsa kudin magani a asibiti ba daga asusun ajiyarsa.

An dai ga jami’an tsaro sun yi dafifi a zagayen bankin, suna kokarin lallashin mutumin.

Kwastamomin da ke cikin bankin yayin faruwar lamarin sun ce Bassam na da Dala 200,000 a asusun bankinsa, amma da ya bukaci cire Dala 2000, bankin ya hana shi.

Kafin mamayar da Bassam ya yi bankin, an ga shi tare da wani dattijo daga Bankin Tarayya na Lebanon da ke Hamra.

Shugaban Sashen Ajiyar kudi na bankin, Hasan Moghnieh, ya bayyana wa kafar yada labarai ta Arab News cewa mutumin ya bukaci ba shi dala 2,000 ne, amma da suka ki ba shi, sai ya bukaci cire kudinsa da ke bankin Dala 210,000.

Ya ce, “Bankin ya yi kokarin ba shi Dala 10,000 madadin hakan, mutumin ya ce allambaram, ya ki karba.

“Yanzu dai ana kokarin kara lallashin sa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa shi dai bai san Bassam ba, amma a tattaunawarsu ya gane cewa Bassam da gaske yake, kuma a shirye yake kowa ya yi asara.

To sai dai mutanen yankin da dama sun nuna goyon bayansu ga matakin da Bassam ya dauka, inda suka dinga ihun Allah wadai da wannan tsarin, daga wajen bankin.

Mutanen na zargin abin da mutumin ya yi sakamano ne na matakin gwamnati da ya sa aka hana cire kudi daga asusun ajiyar bankin miliyoyin mutanen kasar.

Sun kuma yi gargadin cewa irin haka na iya faruwa muddin ba a dauki matakin da ya kamata ba.