’Yan tawaye sun sace Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa maso Yammacin kasar Kamaru, Fon Shomitang II.
Wata majiya daga fadar basaraken ta shaida wa kafafen yada labaran kasar cewa wasu mayakan ’yan a-ware ne suka dauke sarkin daga fadarsa da ke Mbambalang.
- ‘Zan daina neman aikin gwamnati idan na samu N5m’
- An saki mutumin da ake zargi da kisan Jamal Khashoggi
’Yan a-waren da ke fafutukar neman kafa kasa mai cin gashin kanta da ake kira, Ambazonia a yankunan da ke magana da harshen turancin Ingilishi a Kamaru na kai hare-hare kan jami’an gwamnati, manyan mutane da sarakunan gargajiya.
A cewarsu, yin hakan shi ne abin zai tursasa wa gwamnati ta aiwatar da abin da suke bukata.
Sarkin da aka sace dai shi ne shugaban wata kungiya da aka kafa a matsayin wani bangare kan kudurorin tattaunawa saboda matsayi na musamman ga yankunan da ke magana da turancin Ingilishi.
Gwamnatin Kamar ce ta kirkiri kungiyar bayan babbar tattaunawar da aka yi a 2019 da ’yan awaren.
Ga gwamnati, Majalisar Sarakunan ke bayar da sako ko kuma karbar shawarwari daga sarakunan gargajiya da aka ce an dade ana watsi da su wajen yanke shawara a yankunansu na asali.
Sai dai duk da haka an kasa samun matsayar da ake fata a idanun ’yan a-waren.