Hukumar Kula da Gandun Daji ta Jihar Borno ta ce, wasu giwaye da ake zargin sun fito ne daga kasar Kamaru sun mamaye wasu gonakin a jihar.
Wani Darakta a ma’aikatar, Ayuba Peter, ya ya ce lamarin ya zama ruwan dare a cikin shekaru biyar da suka gabata a yankin.
“Muna samun rahoton giwaye na lalata gonaki a kananan hukumomin Gamboru/Ngala da Kala-Balge tsawon shekaru biyar da suka gabata.”
“Suna fitowa daga gandun dajin da ke kasar Jamhuriyar Kamaru a wannan lokaci kuma suna yawo, suna yin barna sosai ga filayen noma,” in ji Peter.
- Mutane miliyan 1 ambaliya ta shafa —Zulum
- ’Yan sanda 32 da bindigogi 5 ke tsaron ƙauyuka 200 a Kastina —Dikko Radda
- Ambaliya ta kashe ’yan Boko Haram a Dajin Sambisa
Ya ci gaba da cewa, an kai rahoto ga gwamnatin tarayya domin daukar matakin gaggawa kuma ana bukatar kayan aiki, kamar bindigogi da harsasai, don tsoratar da giwayen su koma inda suka fito.
Peter ya ce kokarin da ma’aikatar ta yi na fuskantar cikas sakamakon ambaliyar ruwa, tare da rashin tsaro a yankunan da ke kan iyakar Najeriya da Jumhuriyyar Kamaru.
Don haka ya yi kira da a hada karfi da karfe da masu ruwa da tsaki, ciki har da kungiyoyi masu zaman kansu, don kare wannan barazana gaba daya.
Ya kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta bai wa manoma tallafin kudi, musamman wadanda giwayen suka lalata gonakinsu.
A wata wasika da ya aike wa Gwamna Babagana Zulum, wani shugaban al’umma, Baba Hassan daga Ngala, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa don magance matsalar.
Hassan ya nuna damuwarsa kan yadda manoman yankin suka yi asarar miliyoyin Naira, sakamakon barnar wadannan giwaye.
“Mamayar da giwaye suka yi a gonaki a baya-bayan nan ya yi sanadiyar lalata kadada mai yawa na amfanin gona da masu su ke dogaro da su domin rayuwarsu.
“Ka yi tunanin irin halin kaka-nika-yi da rashin da wadannan mutane ke ciki yayin da wadannan giwaye ke cinye gonakinsu.
“Dole ne gwamnati ta sa baki don kawo karshen wannan matsala, wacce ke barazana ga wadatar abinci da tattalin arzikin wadannan al’ummomi.
“A wannan lokaci da aka riga aka fara fuskantar ƙalubale, musamman na tsadar rayuwa, da hauhawar farashin kayan abinci, sai kuma ga wannan abin takaicin ya ƙara tsananta,” in ji Hassan.
Ya ba da shawarar samar da kwararrun ma’aikata don hana giwayen shiga gonaki da shirye-shiryen wayar da kan al’umma kan halayyar giwaye da kare muhalli.
Sauran manoman da abin ya shafa da suka hada da Bunu Modu da Musa Ali na Karamar Hukumar Gamboru/Ngala, sun bayyana mamayar da giwayen suke yi a gonakinsu a matsayin abin takaici.
Har ila yau, Allamin Hassan da Hala Idris, sun ce sun yi hasara mai yawa a gonakinsu sakamakon wannan barna ta giwaye, inda suka yi kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya da su dauki matakan gaggawa don kawo karshen lamarin.
A cewarsu, sai an yi wani abu cikin gaggawa kafin a tilasta wa wadannan giwaye ficewa daga gonakin nasu don samun sa’ida.