✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya sumar da tsohuwar matarsa da duka

Wani mutum ya yi wa tsohuwar matarsa duka har ya sumar da ita a Jihar Legas.

Wani mutum ya yi wa tsohuwar matarsa duka har ya sumar da ita a Jihar Legas.

’Yan sanda sun cafe mutumin ne bayan da matar ta kai musu rahoto samkamon dukan kawo wuka da raunuka tada tsohon mijin nata ya yi mata.

Mutumin ya bi ta ne a lokacin da take hanyar zuwa kasuwa ya yi mata tambaya, amma da ta ba shi  amsar da bai ji dadi ba, sai ya fusata, ya yi mata dukan Kawo wuka.

Kakakin ’yan sandan jihar Legas, Benjamin Hendeyin, ya ce jama’ar da suka kwace ta da kyar ne suka kai ta caji ofis jina-jina, aka garzaya da ita zuwa asibiti.

“Ta shaida mana cewa tsohon mijin nata ya tsayar da ita ne ya tambaye ta game da ’ya’yansu.

“Amsar da ta ba shi ne ya fusata shi, ya lakada mata dukan kawo wuka,” in ji shi.