Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutum shida ’yan gida daya da ake zargin su da yi wa alkalin wata babbar kotu dukan kawo wuka.
Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mahdi Mu’azu Abubakar, ya bayyana cewa ana shigar da karar wadana ake zargin ne a gaban kotun alkalin da suka lakada wa duka, kan shari’ar filin gona.
A cewar sanarwar, daya daga cikin wadanda ake karar ne ya jagoranci ’yan uwansa suka kai wa alkalin da ma’aikatansa duka a lokacin da suka je duba gonar da ake shari’ar a kanta a garin Potuki da ke yankin Degri ba Karamar Hukumar Balanga.
Yayin zantawa da Aminiya, daya daga cikinsu ya bayyana cewa suna cikin gona suna aiki ne kawai suka ga mutane sama da 30 suna zagaya gonar, kuma ba su san kowa a cikinsu ba, sai ’ya’yan kawunsu biyu da suke shari’ar gonar da su, kuma kotu ba ta fada musu cewa za a zo duba gonar ba.
- Daya daga daliban jami’ar da aka sace a Katsina ta kubuta
- Kotu ta sake bayar da belin Emefiele kan miliyan 300
Abubakar Umaru, ya ce ganin mutanen da yawa da wadannan ’yan uwan nasu da suke rikicin gonar da su, ta sa zuciya ta debe su suka kai musu hari suka ji musu ciwo ba tare da sanin akwai alkali a cikinsu ba.
“Mun saba ganin mutane suna zuwa gonarmu haka suna dubawa daga karshe kawai sai mu ji an sayar, ba yadda muka iya, shi ya sa a wannan karon ba mu bari ba, muka tarwatsa su” in ji shi.
A cewarsa, daga baya ne suka gane akwai alkali a cikin mutanen, wanda hakan ya sa suka yi nadamar abin da suka aikata.
Abubakar, ya roki alkalin da sauran da mutanen da su yafe musu kuskuren da suka yi.
“Wannan shari’ar gadar ta muka yi, domin daga rasuwar mahaifinmu ko addu’ar kwana uku ba a yi ba wadannan ’yan uwa namu suka kawo mana sammaci a kan cewa mun gaji shari’ar da suke yi da mahaifinmu kan gonar gado tun da shi ya rasu,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba 2023 ne mutanen suka yi wa alkalin babbar kotu ta da ke garin Gombe dukan kawo wuka.