✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya soki jihohin Yarbawa kan watsi da noma

Manoman Arewa sukan shafe sama da kilomita 700 zuwa 100 su zo Legas.

Wani masani kuma mai sharhi al’amuran yau da kullum a ƙasar nan ya yaba kan yadda manoman Arewa ke ƙoƙarin ciyar da Kudu duk da nisan da ke tsakanin yankunan biyu, inda suke yin safarar kayan abinci, musamman kayan lambu.

Masanin mai suna Dokta Solomon Ẹkúndayọ ya kuma yi kira ga gwamnonin yankin Kudu su tashi tsaye tare da mayar da hankali wajen noma, musamman na kayan lambu da ake da buƙata a kullum a yankin.

“Manoman Arewa da ke da nisa ba su damu da nisan ba, inda suke shafe sama da kilomita 700 zuwa 100 su zo Legas, su koma da miliyoyin kuɗi. Amma duk da haka jihohi biyar da ke kewaye da Legas sun naɗe hannayensu suna kallo,” in ji shi.

Masanin ya zaburar da mutanen yankin da kuma gwamnatocinsu kan su tashi tsaye, su kula da harkar noma, la’akari da irin albarkar da yankin ke da shi da kuma ɗimbin kuɗin da suke karɓa daga Gwamnatin Tarayya.

“Babu wata jiha a Kudu maso Yamma da ba za ta samu sama da Naira biliyan 30 a kowane wata ba a matsayin kuɗin shiga, idan har za ta iya yin amfani da kusancinta da Legas.

Muna zaune a kan dubban hektoci na ƙasar noma, ƙasa mai albarka, amma a banza! A kullum ana yanka shanu kimanin 10,000 a Legas. Mu yi amfani da Naira 400,000 a matsayin ma’auni. Wato Naira biliyan 4 ke nan a kullum da Naira biliyan 120 a kowane wata. Mene ne kiwo da ba za mu iya yi a Kudu maso Yamma ba don cin gajiyarsa.

“Baya ga Legas, Jihar Ekiti ita ce jiha mafi ƙanƙanta a Kudu maso Yamma, muna da hekta 300,000 na gonakin noma, inda Jihar Oyo ta fi mu faɗin ƙasa sau biyar, amma muna zaune ba mu yi komai. Wannan babban abin kunya ne,” in ji shi.

Duk da cewa yankin ba ya da faɗin ƙasa, kamar Arewa, masanin ya ce, yankin zai iya kamo Arewa wajen samar da abinci idan suka haɗa ƙarfi da ƙarfe.

“Ban da Legas, idan muka haɗa yawan faɗin ƙasa na sauran jihohi biyar na Kudu maso Yamma, yankin na da faɗin ƙasa sama da murabba’in kilomita 74,000.

Hekta ɗaya filaye tana kusan kadada 2.5, saboda hekta ɗaya za ta ba ka buhun shinkafa 50. Hekta ɗaya za ta ba ka buhun gari 100. Za mu iya tunanin adadin tumatir da barkono da za mu iya samu daga kadada ɗaya kawai. Amma duk da haka muna da hekta miliyan uku,’’ in ji shi.

Mai fashin baƙin ya ce, duk jihohin da ke Kudu maso Yamma gaba ɗaya suna da ƙananan hukumomi 137.

Baya ga Jihar Kano, Jihar Oyo ce ta fi kowace yawan ƙananan hukumomi a Nijeriya. Sannan ƙananan hukumomi su ne mataki na uku na gwamnati kuma suna karɓar kaso mai tsoka, baya ga kuɗin shiga na cikin gida.

“Mu yi amfani da Naira miliyan 300 a matsayin matsakaicin kason kowane wata. Abin da 137 daga cikinsu ke tarawa kusan Naira biliyan 41 ne. Sannan akwai ƙananan hukumomi a Kudu maso Yamma da ke karɓar kusan Naira biliyan