Shugaban kungiyar Malaman Makarantun Allo na karamar hukumar Jama’a da ke kudancin Jihar Kaduna Malam Mu’azu Usman Guruza ya yi kira ga malaman da ke tafiye-tafiye da almajiransu musamman a irin wannan lokacin da su rika bai wa jami’an tsaro hadin kai idan sun tsare su a hanya.
Shugaban, ya yi wannan kiran ne yayin zantawarsa da Aminiya a garin Kafanchan inda ya bayyana cewa kungiyarsu ta dukufa ka’in da na’in wajen wayar da kan malamai da almajirai muhimmancin zaman lafiya da bin doka da oda a duk inda suka tsinci kansu da kuma mallakar katin shaidan zama dan kasa da na zabe.
Shugaban, ya kuma bayyana cewa kungiyarsu, wacce take reshe ce karkashin shugabansu na Jihar Kaduna Malam Musa Kawo, tana taimakawa tare da shiga tsakani idan wani abu ya kai wani malamin makarantar allo ko wani almajiri hanun hukuma.
“Kamar mu a nan yankin kudancin Kaduna musamman karamar hukumar Jama’a mu kan nunawa bakin almajirai wuraren da ya dace da wuraren da bai dace su rika shiga yin bara ba saboda zaman lafiya. Kafin nan ma yana daga cikin aikinmu tantance duk wasu almajirai da su ka zo domin sanin daga inda su kowannensu ya fito saboda halin yau da gobe.” In ji shi
A karshe malamin yayi kira ga hukumomi da sauran shugabanni da su rika tallafawa irin wadannan kungiyoyi ganin irin muhimmancin da almajirai ke da shi a cikin al’umma saboda karanta littafin Allah da su ke yi a gari da kuma yin addu’o’i da su ke yi don samun zaman lafiya da ci gaban kasa gaba daya sannan yayi addu’a da fatan Allah ya yiwa wannan gwamnati jagoranci bisa ga kyawawan manufofin da ta sanya a gaba.