✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya rasa ransa bayan ya sha maganin yin kudi

Wani dalibin makarantar sakandare, dan shekara 16 da haihuwa, ya halaka a Abekuta, a lokacin da ya kwankwadi wani sinadari da nufin yin siddabaru na…

Wani dalibin makarantar sakandare, dan shekara 16 da haihuwa, ya halaka a Abekuta, a lokacin da ya kwankwadi wani sinadari da nufin yin siddabaru na samun kudi
dalibin mai suna Raimi Fatai, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da suka hada kai da wasu abokansa na makaranta, suka shirya yin maganin kudi. daya daga cikin abokan nasa, dan wani hamshakin boka ne a Jihar Ogun, shi ne ya je musu da bayanan yadda ake yin maganin kudin a rubuce. Nan take suka ce za su jaraba, suka kuma samu kebabben wuri, suka hada maganin inda Raimi Fatai ya kwankwada, inda nan take yanayinsa ya sauya, ya kwanta rashin lafiya kuma bayan kwana biyu ya ce ga garinku nan.
Aminiya ta kalato cewa, akwai yaro daya daga cikin daliban, wanda shi ma ya sha maganin, yana nan kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai a wani asibitin da aka sakaya sunansa. Tuni dai jami’an ’yan sanda na yankin Adatan suka kame daliban da ke da hannu a harkallar. ’Yan uwan dalibin sun bayyana cewa jami’an tsaro sun ba su gawarsa kuma tuni suka yi mata sutura.
Shugabar makarantar, wacce aka sakaye sunanta, ta kira taron gaggawa da iyayen daliban makaranta, a inda ta bayyana sallamar daukacin daliban da ke da hannu a lamarin. Ta shaida cewa kodayake ba a cikin makarantar daliban suka yi wannan aika-aikar ba, duk da haka ta dauki tsauraran matakai don hana afkuwar haka a nan gaba. Ta kuma sha alwashin ci gaba da wayar wa dalibai kai a kan illar sanya kawunansu cikin tsaka mai wuya da nufin yin maganin kudi.
Jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Jihar Ogun, ASP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma shaida cewa rundunar na gudanar da bincike.
Garin Abekuta dai ya yi kaurin suna wajen tsubbace-tsubbace, yana kuma samun halartar dinbin masu musu neman maganin siddabarun yin kudi.