✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu bayan an doke shi da kwallo a kirji

Wani abin takaici ya faru a kasar Kuroshiya a makon jiya in da wani dan kwallo mai suna Bruno Boban mai shekara 25 ya rasu…

Wani abin takaici ya faru a kasar Kuroshiya a makon jiya in da wani dan kwallo mai suna Bruno Boban mai shekara 25 ya rasu bayan an doke shi da kwallo a kirji  lokacin da suke wasan kwallon kafa.   

Jaridar The Sun wacce ake wallafawa a Ingila, ta ce dan kwallon ya rasu ne a lokacin da yake cikin buga wa kulob dinsa kwallo. Ana cikin kwallo ne sai wani ya narka masa kwallo a kirji inda nan take ya zube kasa.

An ce minti 15 kacal da fara wasa ne al’amarin ya faru inda wani ya takura ya narka masa kwallo a kirji.  Likitocin da suke kula da ’yan kwallon sun kwashe minti 40 a kansa kafin ya farfado.

Bayan ya farfado sai ya sake komawa fili, amma cikin kankanen lokaci ya sake zubewa kasa, kuma nan take rai ya yi halinsa.

Takwarorinsa da ke wasan tare da shi ne suka sanar da jami’ansu halin da ake ciki, inda aka garzaya da shi asibiti kuma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Takwarorinsa da jami’an kulob din biyu suka kadu game da faruwar lamarin, kuma sun mika sakonnin ta’aziyarsu ga iyalan mamacin.

Lamarin yana zuwa ne bayan kimanin mako uku da Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Fiorentina da ke Italiya Dabide Astori ya rasu a lokacin da yake kwance yana barci.