✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu a lokacin da yake kwallon kafa

Wani abin mamaki ya faru a kasar Gabon a karshen makon jiya bayan da wani matashi dan kimanin shekara 30 mai suna Herman Tsinga ya…

Wani abin mamaki ya faru a kasar Gabon a karshen makon jiya bayan da wani matashi dan kimanin shekara 30 mai suna Herman Tsinga ya yanke jiki ya fadi a daidai minti na 23 a lokacin da yake buga wasan kwallon kafa.

Herman Tsinga ya rasu ne a lokacin da aka ga ya yanke jiki ya fadi ana tsakiyar wasa a yayin gasar rukunin ’yan dagaji na kasar Gabon.

Rahotanni daga kasar sun ce takwarorinsa da suke kwallo tare sun dauka wasa yake yi lokacin da suka ga ya fadi, amma da suka lura sai suka ga yana shure-shure kumfa na fita daga bakinsa yayin da idanunsa suka kafe.

Nan take suka sanar da likitocin da ke duba lafiyarsu  amma kafin a garzaya da shi asibiti rai ya yi halinsa.

Jaridar The Union Daily da ake wallafawa a kasar ta ce matashin yana buga wa kulob din Akanda FC wasa ne, kuma a ranar da al’amarin ya faru suna karawa ne da kulob din Missile FC.

Sai dai rahotanni sun ce dan kwallon ya kamu ne da matsalar bugun zuciya kamar yadda likitan da ya duba shi a filin kwallon ya tabbatar.

Rahoton ya ce motocin da aka girke a filin wasan don kai ’yan kwallo asibiti idan taimakon gaggawa ta taso, ba su da isassun kayan aiki a ciki wanda hakan ya sa dan kwallon ya rasu tun kafin a kai shi asibiti.

Wannan shi ne karo na bakwai da ’yan kwallo suke yanke jiki su fadi kuma su mutu a yayin da suke yin kwallo a Gabon. Hakan ya sa mutanen kasar ke kira ga mahukuntan kasar su dauki mataki don ganin an tsayar da faruwar lamarin.

Kimanin wata takwas ke nan da aka fara gasar rukunin ’yan dagaji a Gabon kuma kawo yanzu an shiga zagaye na biyu.

Jama’a da dama sun aika sakonnin ta’aziyya ga iyalan mamacin.