’Yan sandan Holland sun
ce, sun samu wani mutum da ya makale a tayar wani jirgin sama da ya tashi tun daga Afirka ta Kudu ya sauka a Amsterdam da ke kasar a raye.
Jiragen sama dai na tafiyar sa’a 11 daga Johannesburg zuwa Amsterdam, kuma
wannan jirgin na dakon kaya ana ganin ya yada zango sau daya ne kawai a Nairobi a kasar Kenya.
- Yadda tsayi ko gajartarka za su iya shafar lafiyarka
- Za a fuskanci hazo da kurar da za su iya hana jirage tashe a Arewa – NiMet
“Abu ne mai wuyar gaske ga mutumin da ya makale a tayar jirgin sama ya rayu a doguwar tafiya, saboda tsananin sanyi
da kuma karancin iskar shaqa a sama. Ba a riga an gane shekaru da kasar mutumin ba,” inji ’yan sandan.
Kakakin ’Yan sandan Holland, Joanna Helmonds ta bayyana wa Kamfanin
Dillancin Labarai na AFP cewa: “An samu mutumin da ransa a ramin tayar gaba na jirgin, kuma an dauke shi zuwa
asibiti cikin hayyacinsa.
Ta ce, “Abu ne mai matukar ban-mamaki ganin cewa, mutumin yana raye, yanzu dai ana kula da shi a asibiti.”
Ta kara da cewa, ana sa ran mutumin zai nemi mafaka a Holland, amma dai abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne
kula da lafiyarsa.
Kakakin Kamfanin Jirgin Saman Dako na Cargolux na Italiya, ya tabbatar wa
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, jirgin wanda ya taso daga Johannesburg zuwa filin jirgin Schiphol da ke Holland ya yada zango a Nairobi.
Abin da ba a sani ba shi ne ko a Afirka ta Kudu mutumin ya makale a jirgin ko a Kenya, yanzu dai ’yan sanda suna
gudanar da bincike a kai.