✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kona makaranta bayan sace mata kwamfutoci a Binuwai

Wanda ake zargi ya banka wa makarantar wuta ne domin kawar da hankalin jama'a.

Wani mutum da ake zargi ya kona wata makarantar firamari bayan ya sace mata kwamfuta ya shiga hannun ’yan sanda.

Lamarin ya faru ne a yankin Moi-Igbo cikin Karamar Hukumar Mbalom a Gwer ta Gabas a jihar.

’Yan sanda sun ce ya aikata hakan ne domin kawar da hankalin jama’a daga kwamfutocin makarantar da ya sace.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar hakan, tare da cewa za su tsananta bincike kan batun.

Ta ce da ma wanda ake zargin ya yi kaurin suna wajen aikata manyan laifuka a yanki.

Kuma ya kona makarantar ce domin jama’a su yi zaton gobara ce ta kama ta kona kwamfutocin da ya sace.

Tuni dai Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko ta Jihar (SUBEB), ta yi tir da wannan danyen aiki.

%d bloggers like this: