Daya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin dake Oko a jihar Edo ya kashe makocin da ya bada shaida akan laifin da ya sa aka daure shi tun da farko jim kadan da tserewarsa daga kurkuku.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar da mutumin ya sami nasarar tserewa daga kurkukun bai tsaya a ko ina ba sai kauyensu inda nan take ya kashe mutumin.
- “Kusan fursunoni 2,000 aka kubutar a gidajen yarin Edo”
- Gwamnatin Edo ta kara wa fursunonin da suka tsere wa’adin kawo kansu
- #EndSARS: An kona ofisoshin ‘yan sanda 2 da na AIT a Edo
- ‘Yan sanda sun gargadi masu tayar da zaune tsaye a Edo da Delta
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Babatunde Kokumo wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mutumin na daya daga cikin fursunoni 1,993 da suka tsere daga bayan fasa kurkukun da wasu bata-gari suka yi.
Babatunde ya ce tuni suka kama mutum masu laifi har guda 126, wadanda goma daga cikinsu wadanda suka tsere ne daga kurkukun.
“Mun ci gaba da tsaurara bincike, kuma mun sake kamo masu laifi 10 da suka tsere daga gidan yari yayin zanga-zangar #EndSARS.
“Daya daga cikinsu, bayan tserewa a ranar ya koma kauyensu tare ya kashe makocinsa da ya bada shaida akansa a kotu.
“Guda uku daga cikin wadanda suka tsere din an kama su ne yayin da suke kokarin kwace wa wani mutum mota kirar Camry”.
“An yi nasarar sake cafke su tare da makaman da suka tsere dasu”, inji kwamishinan ‘yan sandan jihar,” inji kwamishinan.
Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne wasu zaune-gari-banza suka fasa gidan yarin na jihar Edo da sunan zanga-zangar #EndSARS tare da saki fursunoni da dama ciki.