✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe matarsa ya binne ta a gidansa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wani magidanci mai suna Aminu Inuwa bisa zarginsa da kashe matarsa tare da binne gawarta a cikin gidansa…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wani magidanci mai suna Aminu Inuwa bisa zarginsa da kashe matarsa tare da binne gawarta a cikin gidansa a Unguwar Jakada,  yankin Dorayi cikin birnin Kano.

Wata majiya ta ce magidanci y’a kashe matar tasa mai suna Safara’u Aminu ta hanyar yanka ta da wuka bayan ya kwada mata tabarya a kanta.

Asirin wanda ake zargin ya tonu ne bayan da ya bukaci sanin yadda ake binne gawa daga wani makwabcinsa.

Makwabcin wanda ake zargin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce “Ya zo ya same ni yana ta yi mini wasu zantuttuka yana gaya mini wai matarsa ta bata.  Zuwa can kuma sai ya tambaye  ni yadda ake binne gawa da sauransu. Hakan ya sa na shiga cikin gidan inda na ga ramin da ya binne ta a ciki.  Daga nan na je na sanar wa ’yan sanda.”

Sai dai wanda ake zargin ya bayyana cewa tsautsayi ne ya kai shi ga aikata hakan domin a cewarsa yana matukar son matarsa. “Tsautsayi ne ya sa na aikata haka, muna son junanmu ni da ita. Idan ma akwai abin da ke hada mu rigima shi ne yadda ba ta yi mini biyayya,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP  Haruna Abdullahi ya tanbbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin yana hannunsu kuma suna ci gaba da bincike idan sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kotu.