✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe masoyiyarsa da ’ya’yanta saboda ta rabu da shi

Shi ma ya mutu bayan da ya cinna wa gidanta wuta da tsakar dare

Wani mutum ya cinna wa gidan masoyiyarsa wuta ya kuma aika ta lahira tare da ’ya’yanta biyu.

Wasu ’ya’yan matar su uku kuma sun samu mummunar kuna a sakamakon wutar da mutumin ya sa wa gidan da tsakar dare, inda a halin yanzu ake jinyar su a Asibitin Anglican, Molete.

Matar tsohuwar daduron mutumin da ake zargi da kashe ta ne a unguwar Idi-Arere na garin Ibadan, Jihar Oyo.

Suna tsaka da zamansu na daduro ne ta rabu da shi, matakin da ya fusata shi, ya kai shi ga yin barazanar kashe ta; Daga baya ya faki ido cikin tsakar dare ya yi aika-aikan.

Wanda ake zargin, shi ma ya yi mummunar kuna a sakamakon wutar da ya cinna wa gidan, wadda kuma ta yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin ’yan sandan Jihar Oyo, CSP Olugbenga Fadeyi, ya ce, “Zaman daduro suke yi; mutumin ya kona gidan tsohuwar farkar tasa ne saboda ta nemi rabuwa da shi.

“Wutar ta kashe matar da ’ya’yanta biyu; shi ma mutumin ya mutu daga baya, sauran yara uku da suka samu rauni kuma ana jinyar su a asibiti.”

Ya ce ’yan sanda na gudanar da bincike kan abin da ya faru domin gano hakikanin lamarin.