✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe makwabcinsa don gudun biyan bashi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta damke wani mutum kan zargin kashe makwabcinsa da ke bin sa bashi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta damke wani mutum kan zargin kashe makwabcinsa da ke bin sa bashi.

Mai magana da yawun rundunar, Adewale Osifeso, ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin ya kashe makwabcin nasa ne don kubuta daga bashin da yake bin sa.

Ya ce bayan kashe marigayin, wanda ake zargin ya dauki motar da ya bayar a matsayin jingina na bashin da ya karba ya tsere da ita.

Da yake bayani sa’ilin da suke gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a ranar Talata, Osifeso ya ce wani mai suna Adesope Adeolu ne ya kai rahoto ofishin ’yan sanda da ke Eleyele bayan faruwar lamarin cewa ya ga kofar makwabcinsa a bude, wanda bai saba aukuwa ba.

“Ko da ya bincika, sai ya tarar da makwabcinsa Olusegun Rufus, kwance cikin jini a mace, inda ya yi zargin mai yiwuwa kashe shi aka yi,” inji jami’in.

Ya ce bayan bincike da bayanan sirri da aka tattara, aka kama wanda ake zargin wanda ya tabbatar shi ne ya kashe Rufus don ya kubuta daga bashin da yake bin sa.

“Haka nan, an gano motar da ya jinginar don karbar bashin wadda ya yi amfani da ita ya tsere,” in ji shi.