’Yan sanda a Jihar Neja sun damke wani matashi kan zargin yin sojan-gona a matsayin jami’in soja a garin Ibeto cikin yankin Karamar Hukumar Magama a jihar.
Da suke baje kolin wanda ake zargin a Minna babban birnin jihar, Mai Magana da yawun ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an samu wanda ake zargin da wasu kayan sojoji da kudi Naira 720,00 da mota kirar Marsandi da sauran.
Ko da yake dai wanda ake zargin, wanda dan asalin Wawu-Garin Warra a Karamar Hulumar Ngaski, Jihar Kebbi, ya musanta zargin.
Ya ce kayan sojojin da aka same shi da su na wani dan uwansa ne da ke soja wanda ke aiki a Warri, babban birnin Jihar Delta.
Abiodun ya ce da ma wanda ake zargin na daga jerin mutanen da suke nema tun bayan da ya ajiye wata mota kirar Honda Accord a Maje da ke hanyar Kontagora a 2020 don guje wa kamun hukuma.
Ya kara da cewa, “Ya kasa ba da cikakken bayani game da kansa, ya ce shi dillalin motoci ne kuma manomi.
“Ya ce kudin da aka same shi dauke da shi, na sayen mota ne.”