Rundunar ’yan sandan jihar Filatu ta cika hannunta da wani fasto da ake zargi da karyar an sace shi, ya kuma karbi kudin fansa daga mabiyansa.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Alabo Alfred, ya fitar ranar Laraba a Jos, ya ce an kama faston ne tare da wasu mutane uku da ya hada baki da su a matsayin wadanda suka sace shi.
“Sau biyu yana yin haka da sunan an sace shi. A ranar 14/11/2022, da kuma 30/11/2022 ne mabiyansa suka biya N400,000 da kuma N200,000 a matsayin kudin fansa a lokuta daban-daban, daga nan ne ma suka fara tantamar lamarin.
“Da zancen ya zo gabanmu muka shiga bincike, muka gano ashe hada baki ya yi da wasu matasa uku, da ke boye shi, da kuma yin magana a matsayin wadanda suka sace shi.
“Baya ga haka, ya kuma fada mana ya taba kone motar wani shugabansa a coci ranar 4/1/2023, saboda ya fahimci baya kaunarsa,” in ji shi.
Jami’in ya ce faston da mutum biyu daga cikin abokan cin mushensa suna hannu, guda ya ari na kare, kuma da zarar sun kamo shi za su gurfanar da su a gabana kotu.