Rundunar ’Yan Sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi mai shekara 27 bisa zargin kashe wata yarinya mai shekara 13 a duniya, sannan ya kona gawarta bayan ya yi mata ciki.
Wanda ake zargin, suna Munkaila Ado, wanda tuni ya amsa laifin kashe budurwar tasa mai suna Safiya Alhaji Danladi, ya kuma ce ya binne gawarta a daji daga bisani.
- An kama dan daudun da yake zagin kabarin mahaifiyar abokin fadansa na TikTok
- Gobara ta kashe mutum 41 suna tsaka da ibada a coci a Masar
Ita dai marigayiyar mahaifinta ne tun da farko ya kai rahoton bacewarta, kuma ya ce yana zargin saurayinta Munkaila da abokinsa, Muazu Umar.
Babban wanda ake zargin, Munkaila Ado, ya bayyana cewa Safiya da ta bace budurwarsa ce, kuma tana dauke da cikinsa kimanin wata hudu, kuma mahaifiyarta ta sani, amma mahaifin, Alhaji Danladi Mohammed bai sani ba.
Ya kuma ce ya hada baki ne da mahaifiyar yarinyar da ta bace da kuma abokin aikinsa, Muazu Umar, inda suka tafi da wacce aka kashe din zuwa Gombe don a zubar da cikin.
Munkaila ya ce da isarsa Gombe aka kai ta gidan wata mata Hajiya Amina Abubakar mai shekara 50 da haihuwa a unguwar Jekada Fari bayan asibitin kwararru da ke Gombe inda aka zubar da cikin.
Ya kara da cewa an ba wa Safiya wasu sinadarai da ke haifar da zubewar ciki amma daga karshe a kan hanyarsu ta zuwa kauyen Mai’ari da ke kusa da karamar hukumar Akko Jihar Gombe, Munkaila da abokinsa sun yanke shawarar kashe ta kuma suka aikata hakan.
Wanda ake zargin ya ci gaba da cewa, Safiya ta fadi a sume ta mutu, shi da abokin nasa kuma suka kona gawarta, sannan suka binne ta a wani kabari mara zurfi a wani daji da ke kusa da karamar hukumar Akko ta jihar Gombe.
Jami’an ’yan sanda sun kama mutanen biyu da ake zargin.
Tuni dai Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Bauchi, Umar Sanda, ya nuna bacin ransa a kan lamarin, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.
A cewar wata sanarwa da rundunar a jihar ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, SP Ahmed Mohammed Wakil, ta ce tun fari mahaifin marigayiyar, Alhaji Danladi Mohammed na kauyen Mai’ari Arewa da ke gundumar Pali ya kai kara a hedkwatar ’yan sanda ta Alkaleri a ranar 10 ga watan Agustan 2022 kan batan diyar tasa.
Mahaifin yarinyar ya ce tun ranar hudu ga watan Agustan 2022 ’yar tasa ta bace.
Mahaifin marigayiyar ya ce Munkaila da Mu’azu yake zargi da hannu a batan nata.
Kakakin ’yan sandan dai ya ce da samun koken aka kama wadanda ake zargi kuma babban jami’in ’yan sanda na Alkaleri ya ziyarci inda lamarin ya faru, inda suka tono gawarta suka kai ta zuwa babban asibitin Alkaleri inda likita ya tabbatar da mutuwarta.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da bincike kamar yadda kwamishinan ya bayar da umarni ga sashen binciken manyan laifuka na jiha (SCID) domin gudanar da bincike mai zurfi.