✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe alkalin wasa saboda jan kati

Wani abu mai kama da almara ya faru a kasar Meziko a karshen makon jiya bayan wani dan kwallo ya lakada wa wani alkalin wasa…

Wani abu mai kama da almara ya faru a kasar Meziko a karshen makon jiya bayan wani dan kwallo ya lakada wa wani alkalin wasa duka saboda ya ba shi jan kati (Red card) da hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Jose bildmar Hernandez Capetillo shi ne alkalin wasan da ya rasa ransa bayan ya kwashe kimanin kwanaki bakwai a wani asibiti yana sume sanadiyyar dukan da dan kwallon ya yi masa saboda  jan kati a lokacin da wasan kwallon kafa ke gudana.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta The Sun News ta kalato, an nuna alkalin wasan ya rasu ne bayan ya kwashe kwanaki 7 a sume bai san inda yake ba, inda daga baya ne ya ce ga-garinku a wani asibiti.

Kamar yadda rahoton ya nuna, al’amarin ya faru ne a lokacin da ake buga wasan rukunin ’yan dagaji a Gabashin Meziko a wani filin wasa da ake kira Premid-El-Castillo.  Ana cikin tsakiyar wasa ne sai wani daga cikin ’yan kwallon ya yi keta da hakan ta sa alkalin wasan bai yi wata-wata ba ya daga masa jan kati.  Ashe al’amarin bai yi wa dan kwallon dadi ba, inda nan take ya zabga masa karo kuma ya shiga jibgarsa har sai da ya fadi kasa warwas. 

Kafin ka ce kwabo filin ya yamutse yayin da wasu ke kokarin kai wa alkalin wasan dauki wasu kuwa suna kara rura wutar rikicin ce.

Bayan da alkalin ya suma ne sai dan kwallon ya sulale ba tare da sanin kowa ba daga nan ne aka garzaya da alkalin wasan zuwa wani asibiti mafi kusa. Alkalin ya shafe kimanin kwanaki 7 a asibitin a sume kafin ya rasu.

Shugaban kungiyar alkalan wasa ta Meaziko balentin Ramirez ya tabbatar da aukuwar wannan lamari kuma ya nuna takaicinsa game da faruwar wannan lamari inda ya ce yana fata jami’an tsaro za su kamo dan kwallon da ya aikata haka don ya fuskanci hukunci.

An ce dan kwallon ya bi wata motar dakon kaya ce wajen arcewa bayan da ya fahimci an kira jami’an tsaro da hakan ta sa ya zuwa hada wannan rahoto ba a yi nasarar kama shi ba.