✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe abokinsa saboda musun shekarun haihuwa

Gardama ta kaure tsakanin wasu abokai har ta yi sanadiyyar kisa.

Gardama ta kaure tsakanin wasu abokai biyu kan yawan  shekaru, har ta yi sanadiyyar bugu zuwa kisa.

Daya daga cikin abokan mai suna Levison Luphahla mai shekara 32 daga kauyen Geleza a birnin Lupane na kasar Zimbabwe ya fusata  ne bayan musun ya kaure tsakaninsa da abokinsa mai suna Khumbulani Tshuma mai shekara 30, da ya yi ikirarin cewa ya girmi Levison.

Hakan ya sa Levison ya yi fushi da abokin nasa saboda ya yi ikirarin shi  ne na gaba da shi a shekaru. saboda haka ya afka masa da duka, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Khumbulani.

A cewar majiyar Chronicle, abokan su biyu sun kaure da musun ne lokacin da suke shan giyar gargajiya, sai musun ya sauya zuwa rikicin da ba za a iya sasantawa ba.

Ana cikin hakak ne sai Khumbulani ya kwada wa Levison Luphahla katakon kujera a fuska, ya kuma yi gaba.

Shi kuma Levison sai ya fusata ya tunkare shi don yin fansa, inda ya kwada masa gungumen icce bayan rike shi.

Levison ya koma gida bayan barin Khumbulani a kwance a fegin noman masara, a cikin daren da abin ya faru kuma Khumbulani ya mutu.

An dai kama Levison kan laifin kisan kai, aka kuma gurfanar da shi a babbar kotun Bulawayo wanda mai shari’a Martin Makonese ke jagoranta.

Sai dai bai amince da laifin da ake zargin sa ba kan kisan kai.

Alkalin kotun ya fahimci cewa Levison yana cikin maye a lokacin da ya aikata laifin, sannan an yanke masa daurin shekara hudu a gidan yari.

Mai shari’a Makonese ya rage wa’adin zaman gidan yarin da shekara daya, a maimakon shekara biyar da aka yanke masa saboda halinsa mai kyau da yake da shi a baya.

Hakan na nuna cewa, Levison zai yi zaman gidan yarin na tsawan shekara hudu.