✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata matasa su rungumi sana’o’in hannu —Murtala Gwarmai

Alhaji Gwarmai ya sama wa wasu matasa 8 aikin yi a Ma’aikatar Lafiyar Kano

Hadimin Gwamnan Kano na Musamman kan Harkokin Matasa, Alhaji Murtala Salisu Gwarmai, ya bukaci matasa da su yi watsi da zaman kashe wando ta hanyar rungumar sana’o’in hannu ko da kuwa sun yi karatun boko.

Alhaji Gwarmai ya dole sai matasa sun tashi tsaye wajen neman abun dogaro da kai sannan za su tsira da mutunci.

Hadimin gwamnan na wannan tsokaci yayin da yake jawabi ga wasu matasa da ya samawa aikin yi a Ma’aikatar Lafiya ta Kano

Da yake mika takardun daukar aikin, Murtala Gwarmai ya ce ya samo mu aikin ne a kokarinsa na sauke nauyin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dora masa na ganin rayuwar matasa a Jihar kano ta inganta.

“Mutane da dama sun yi irin karatun da kuka yi amma ba su taki irin wannan sa’a ta samun aikin din-din-din a gwamnatin jiha ba, don haka nake horon da ku rike wannan aikin da kyau,” a cewar Gwarmai

Gwarmai wanda ya ce ba wannan ne farau ba, yana alfahari da kokarin da yake yi na ganin matasa sun samu abin dogaro da kai.

A cewarsa, “duk matasan da suka yaki zaman banza, wata rana za su taimaki wasu wanda da haka sai a kaga an tallafa wa matasa masu tarin yawa.

Gwamnati ba za ta iya sama wa kowa aiki ba, don haka nake kira ga matasa da su rungumi kananan sana’o’in hannu domin su dogara da kawunansu ko da kuwa sun yi karatun boko.

Akalla dai matasa guda 8 ne maza da mata suka samu aikin a Ma’aikatar Lafiya sanadiyyar Alhaji Murtala Salisu Gwarmai

Wasu daga cikin wadanda suka samu aikin sun gode wa Allah da wannna dama da suka samu, tare da gode wa Murtala Gwarmai bisa wannan abun alheri da ya yi musu.

Rahotanni sun ce Murtala Gwarmai ya sama wa matasa aiyukan yi a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Jihar Kano daban-daban.