✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata mata su koyi aikin likita  – Sabuwa Birnin Kudu

Hajiya Sabuwa Salihi Sulaiman Birnin Kudu fitacciyar ma’aikaciyar asibiti ce da ta yi  suna wajen kula da marasa lafiya a Babban Asibitin Birnin Kudu da…

Hajiya Sabuwa Salihi Sulaiman Birnin Kudu fitacciyar ma’aikaciyar asibiti ce da ta yi  suna wajen kula da marasa lafiya a Babban Asibitin Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara aikin jinya da yadda yanayin aikin ya koma a yanzu:

 

Tarihina Sunana Hajiya Sabuwa Sulaiman Salihi Birnin Kudu. An haife ni a nan garin Birnin Kudu a Kofar Fada. Na yi makarantar firamare ta Birnin Kudu da firamaren Yakubu Palace, inda na gama a 1974 lokacin ana yin aji bakwai.

Na yi aure bayan na gama firamare da shekara uku wato a 1977. Kuma ina da shekara 11 da aure a lokacin muna da ’ya’ya shida mijina ya sa na shiga Makarantar Kiwon Lafiya ta Birnin Kudu,  na yi kwas din  karamar malamar jinya (Clinical Assistance) da na gama sai aka tura ni Asibitin Murtala da ke Kano. Da yake ina da aure sai mijina ya je Ma’aikatar Lafiya ya nema min canji aka dawo da ni Asibitin Birnin Kudu na dawo na ci gaba da aiki.

 

A lokacin mene ne aikinki?

A wancan lokacin saboda karancin ma’aikatan lafiya za ka ga mata ne suke kula da marasa lafiya wani wurin kuma maza ne suke duba maza. A wancan lokacin mu ne muke yi wa marasa lafiya wanka a kan gadonsu mu juya su, mu shafe musu jikinsu da mai kuma mu ne muke wanke musu gyanbonsu. Saboda a wancan zamanin akwai yawaitar ciwon gyambo, haka muna yin allura da sa wa marasa lafiya ruwa ko karin jini.

 

Yaya tsarin aiki yake a wancan lokaci?

A gaskiya komai yana tafiya a tsare babu yadda na kasa zai taka na sama kuma komai dare in aka kawo marar lafiya aka sanar da likita an kawo marar lafiya ko da ya kwanta barci zai taso ya zo ya bada agaji wajen ceton marar lafiya ba tare da an samu wata matsala ba.

 

Da yake kin jima kina aikin jinya kasancewar aiki ne da yake bukatar karance-karance ko kin samu damar kara karatu?

A’a ban samu wata dama ta kara karatu ba, ni daga aji bakwai na firamare da na yi sai kwas na Clinical Assistance da na yi daga shi ban je wani karatu ba.

Amma in ka yi la’akari da karatu irin na wancan zamani darajar karatun a yau tamkar diploma za a ce.

 

Yanzu mene ne matsayinki a aikace ?

Matsayina ni ce Babbar Jami’ar Nas (Chief Nursing Officer) a Babban Asibitin Birnin Kudu kuma ina mataki na takwas na aiki.

 

Daga lokacin da kika fara aiki zuwa yau me ya fi ba ki tausayi a aikinki na kiwon lafiya?

Babu abin da ya fi ba ni tausayi kamar yadda wata rana wata mata Bafilatana hadari ya rutsa da ita a wata motar dakon siminti. Siminti ya fada musu a ka ita da ’yarta, yarinyar ta rasu ita kuma ta kakkarye ta ji raurunuka aka kawo ta asibiti. A lokacin da aka kawo ta na ji tsoron taba ta sai ta ce min malama ni mutum ce kada ki ji tsoro. Jin haka sai na daure na shiga wanke mata jinin jikinta,  ina cikin wanke mata jikin ne na ga wasu makudan kudi a jikinta. Abin ya ba ni takaici saboda a ce mutum yana da wannan kudi amma yana hawa motar dakon kaya saboda son araha, wannan al’amarin na jima yana min yawo a zuciyata.

 

Mene ne burinki a rayuwa?

Ba ni da wani buri a rayuwa da ya wuce in ga ’yan uwanmu mata sun rungumi harkar kiwon lafiya suna yin karatun aikin likita domin su rika taimaka wa ’yan uwansu mata da ke zuwa asibiti neman lafiya. Saboda haka ne ma idan na yi ritaya nake da burin in kafa asibiti mai zaman kansa saboda in rika tallafa wa matasa a fannin kiwon lafiya, musamman mata masu haihuwa saboda mafiya yawanci za ka ga an kawo mata asibiti inda za ka ga ko gadon da za a kwantar da su babu saboda yawan mata masu haihuwa a kullum. Kuma duk wadda ba ta samu gado ba za ka ga ’yan uwanta sun koma gefe suna zagin ma’aikatan lafiya, alhalin su ma ba laifinsu ba ne, abubuwa ne suke yi wa gwamnati yawa.

 

To yaya kika yi kika koyi aiki har kika iya?

A lokacinmu akwai biyayya ba ma yi wa manya rashin kunya, ba ma kiran sunan manyanmu garan-gatsam sai mun sakaya da malam ko dokta. Haka kuma ba ma zama a kujerunsu sabanin yanzu da mafiya yawan yaran ba sa tsayawa su koyi aiki. Ba sa yi maka magana da biyayya ko tarbiyya. Kai  wadansu ma sai ka ga babba ya tashi sun zauna a kan kujerarsa, haka ba ya cikin tsarin aikimu a zamaninmu.

 

Sau da yawa wadansu na korafin cewa ma’aikatan asibiti suna wulakanta su, shin a zamaninku yaya abin yake?

A gaskiya mu dai ba ma yin haka, kuma wallahi duk wadanda muka koyi aiki a baya ba haka mu ke yi ba. Kuma ko su ma na yanzu an gwada musu sai dai ba sa yin aiki ne da abin da aka gwada musu. An koya mana mu ja marasa lafiya a jikinmu tamkar ’yan uwanmu na jini, mu rika zama da su muna yin hira. Kai a yadda aka karantar da mu ya kamata a ce in su ji sauki an sallame su mu ne za mu raka su, mu sa su a mota zuwa gida. Sabanin yanzu da za ka ga ana fada har da zage -zage a tsakanin ’yan uwan marasa lafiya da ma’aikatan lafiya a wasu wuraren.

 

An ce ba kwa bari ’yan uwan marasa lafiya su gana da su, shi ne ya sa ake yin fada da ku?

Ba haka ba ne, sai dai da yawa da safe ana wanke dakunan marasa lafiya a sa magani don haka ba a son kowa ya shiga har sai an gama. Sannan su kansu marasa lafiyar sai an bukaci lokaci don a gyara musu kwanciya. Saboda haka ne ake ware lokacin ziyara da safe da yamma, amma saboda wadansu ba su san haka ba sai ka ga sun koma suna zagin ma’aikatanmu.

 

Yaya batun kayan aiki a yau a asibitoci?

A gaskiya akwai kayan aiki sosai, sai dai abin da ba a rasa ba saboda nauyi ya yi wa gwamnati yawa tunda jama’a sun yi yawa don haka bukatu sun karu.

 

Yaya batun kwalliya fa?

Ba ni da wata kwalliya a rayuwata da ta wuce in yi ado da atamfa da hijabi ko babban mayafi in rufe jikina, ni shiga nake yi ta mutunci.

 

Me ya fi faranta miki rai a rayuwa?

Babu abin da yake sa ni farin ciki irin in gan ni tare da mijina da yaranmu da kishiyata muna zaune lafiya. Wannan al’amari yana sa ni farin ciki saboda ni da kishiyata muna zaune lafiya. Ta dauki mahaifana iyayenta ni ma kuma na dauki iyayenta iyayena, muna ganin mutuncin junanmu tamkar uwa daya uba daya babu wanda yake jin tsakaninmu.

 

Kin taba yaji daga lokacin da aka yi miki aure zuwa yanzu?

Ban taba yin yaji ba, ban san ma yaji ba. Yau shekarata 42 da yin aure ban taba zuwa gidanmu da sunan yaji ba.

 

A ganinki me ke kawo mutuwar aure a yau?

Ba komai ne yake kawo mutuwar aure ba a yau sai rashin sahihan waliyyai. Duk auren da aka yi ba waliyyai nagari ba ya dadewa yake lalacewa. Har mahaifina ya rasu ban taba kai karar mijina ba, in muka samu sabani da mijina mahaifiyarsa ce take daidaita mu. Kuma ban taba kai karar abokiyar zamata ba. In muka samu sabani mahaifinsa ne yake samu a gaba ya yi mana fada. Wallahi har mahaifina ya rasu bai taba jin wata matsala a tsakanina da mijina ba, ko abokiyar zamana shi ya sa yake sa min albarka.

 

Kina da wani sako ga ’yan uwanki mata?

Kirana ga mata ’yan uwana su tashi tsaye wajen neman ilimin zamani, su koyi aikin likita don taimaka wa mata ’yan uwansu musamman wajen harkar haihuwa inda ake da karancin mata likitoci, wadanda za su duba mata da suke da matsalar haihuwa.