Farida Kabir matashiya ce da ke harkar kimiyyar sadarwa tare da cewa ta karanta fannin kiwon lafiya. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana nasarorin da ta samu da kalubalen da ta fuskanta da yadda ta tsinci kanta cikin harkar sadarwa:
Ilimi
Da yake na yi mafi yawan rayuwa ce a Legas, a can ne na fara karatuna. Na fara ne a makarantar Firamare ta Child Will International daga baya sai aka mayar da ni makarantar Al-Furkan inda na kammala karatun firamare. A lokacin da ake yin hatsaniyar ’ya’yan Kungiyar OPC ta Yarbawa, sai muka koma Kaduna da zama saboda ana yawan kashe-kashe a Legas a wancan lokaci. A Kaduna na zauna da kakata inda na fara zuwa makarantar Mamina Memorial wacce take a Tudun-Wada daga nan ne na shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya na fara karatun digiri a fannin kimiyyar halittu da tsirrai na kammala a 2013.
Kuruciya
Ban zauna da mahaifina ba saosai, domin kafin in girma ya rabu da mahaifiyata, don haka mafi yawan rayuwata tare da kakata na yi saboda mamata ta koma makaranta. Don haka ko da na taso ni ma kaina uwa ce domin ina da kanne hudu wadanda nake kula da su.
Aiki
A halin yanzu ni ’yar kasuwa ce kuma har ilya yau ina aikin kirkirar manhaja ta Intanet. Duk da yake na karanci kimiyyar halittu da tsirrai ne amma dai yanzu na sa hannu cikin ayyukan fasahar sadarwa ne. Domin tun ina karama ina matukar son aikin sadarwa, saboda mahaifina Injiniya ne wanda yake aiki da Kamfanin Sadarwa na MTN a farkon zuwansa Legas. Don haka duk lokacin da na gan shi yana aiki da na’urar kwamfuta nakan zauna in sanya ido a kan abin da yake yi. Har ma ta kai nakan yi masa tambayoyi ya gwada mini wasu abubuwa. Daga nan ne na fara sha’awar wannan aiki nasu. Amma kuma asali ni ina son in zama likita ce, saboda haka ko a lokacin da na gama sakandare, abin da na nema ke nan a jami’a, amma ban yi sa’ar samun yawan makin da suke bukata ba, shi ya sanya suka ba ni fannin nazarin kimiyyar halittu da tsirrai.
Na yi aikin yi wa kasa hidima a Ma’aikatar Lafiya bangaren Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka ta Kasa a Abuja, a wani bangare na aikin ne sai na fara wani aiki mai taken OTRAC a lokacin da aka samu barkewar cutar Ebola na kirkiro wani shafi na Intanet da na sanya duk wasu muhiman bayanai game da cutar ta Ebola da kuma yadda za a yi kariya daga kamuwa daga gare ta. Daga nan ne sai na ga lallai akwai bukatar in ci gaba da wannan fanni na sadarwa.
Sai na fara neman wani kwas da zan yi don in kasance daya daga cikin masu aikin sadarwa. Sai kuwa na ci sa’a na samu wani shiri na karatu kan wannan fanni wanda Kamfanin Google suka dauki nauyi. Haka na yi rajista kuma na yi kwas na wata uku inda daga nan ne ni ma na zama Injiniya ta kirkirar manhajar sadarwa. Sai na ci gaba da hada karatun da na yi da kuma sha’awar yin wannan aiki da nake har na kai ga abin da nake a yanzu.
Yanzu ni ce shugaba na fannin Google Tech Women kuma ni ce jami’ar shirye-shirye ta Google Debelopment Group ta Abuja. Ka san Google yana da mutanensa a ko’ina a duniya wadanda suke tallafa masa wajen ingantawa da tallata fasaharsa da ayyukansa na sadarwa. Ayyukan kowace shugaba shi ne ta tallafa wa mata masu ayyukan fasaha. A lokacin da na kammala samun horona sai na samu wani aikin sa- kai na horo na wata uku a wani kamfani mai suna Hotel.ng da ke Legas. Bayan na kammala sai kuma na samu aiki da wani kamfani mai suna SAMS wanda ke nan Abuja. Ta haka ne na hadu da hadakar masu shirya gamayyar fasaha ta Google na Abuja, wanda a yanzu haka ni ce Jakadiyar Kamfanin Google.
Kalubale
Kowace rana tana zuwa ne da wani sabon kalubale, zai iya zama na iyali ko na kudi da sauransu. Ba zan iya cewa duk na yi maganinsu ba. Amma dai ina bakin kokarina in ga na magance wadanda suka zama tilas. Saura kuma sai in dauke su ta yadda suka zo.
Kololuwar matsayi
Ita ce ranar da tsohon Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande ya mika mini kyautar girmamawa a shekarar 2017 bisa ga kwazon da nake yi a kan abin da ya shafi sadarwa a bangaren kiwon lafiya. An gayyace ni zuwa Bamako na kasar Mali inda shugabannin kasashe ciki har da na Faransa ke gudanar da wani babban taro na kasa da kasa. A lokacin ni kadai ce ’yar Najeriya da aka gayyata. Haka aka kira ni na fito bainar manyan shugabannin duniya na sha hannu da su na karbi kyautata. A nan na ce a raina ‘Mama, bukatar ’yarki ta biya.
Matsayina na mahaifiya
Ina da da wanda nan da zuwa watan Nuwamba zai cika shekara shida, yana nan yana ta kiriniyarsa. Amma wani lokaci mukan dauki lokaci ba mu ga juna ba.
Haduwa da maigida
An gabatar da mu ga juna ne ta hanyar ’yan uwa.
Halayyarsa da na so
Hakuri, shi mutum ne mai hakuri sosai, ba mu taba fada ba a tsawon shekara bakwai da muka yi aure.
Inda na fi son ziyarta
Birnin Paris, birni ne mai kyau kuma akwai zaman lafiya, na taba zuwa har sau biyu. Sannan kuma ina son birnin Disneyland.
Abincin da na fi so?
Tuwo da miyar kuka sai kuma dambun nama.
Wadda nake koyi da ita
Amina Mohammed ita nake koyi da ita.
Yadda nake yin hutu
Nakan yi hutu ne ta hanyar shiga kafafen sadarwa na zamani da wayata ko karamar kwamfuta. Musamman ina ziyartar kafar sadarwa ta Twitter.
Kayan da ba zan taba sanya su ba
Karamin buje wanda zai bayyana kafafuwana a waje
Turaren da na fi so
Shi ne turaren Si na Kamfanin Giorgio Armani.
Shawarar da mahaifiyata ta taba ba ni da ba zan taba mantawa ba
Shawara biyu ce, ta farko takan ce “Farida duk mutanen da suka ci gaba a duniya ba kai biyu gare su ba, daya ne kamar naki. Don haka ke ma za ki iya idan kika dage.” Sai ta biyu takan ce “Ki kasance mai wadatar zuci.”
Shawarar da zan bai wa mata
Su kasansce masu dogaro da kansu, kuma su rika neman shawara. Domin yana da kyau a ce mutum yana da mai sanya shi a hanya. Akwai wata magana wanda na aminta da ita da wani mai suna Richard Brandson ya yi wacce ya ce “Shawara mabudi ce ga duk wani tunani mai kyau kan sana’a.”