✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata dalibai su maka ASUU a kotu —Ministan Ilimi 

Ministan ya ce aiwatar da tsarin Gwamnatin Tarayya na ba-aiki-ba-biya ne kadai ke kawo tsaiko wajen yin sulhu da kungiyar.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ce daliban da yakin aikin Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ya kawo wa karatunsu tsaiko su kai maka kungiyar a kotu su nemi diyyar bata musu lokacin karatu.

Ministan ya fadi hakan ne a jawabinsa game da batun neman biyan diyya ga daliban da yajin aikin na ASUU ya gurgunta harkokin karatunsu.

Adamu Adamu ya ce alhakin ASUU ne ta biya daliban diyya tun kungiyar ce ta rufe makarantun ba gwamnati ba.

Ya bayyana hakan ne a a Fadar Shugaban ranar Alhamis, a lokacin da yake karin haske kan inda aka kwana game da sulhun da Gwamnatin Tarayya ke kokarin yi da kungiyar.

Ministan ya ce aiwatar da tsarin Gwamnatin Tarayya na ba-aiki-ba-biya ne kadai ke kawo tsaiko wajen yin sulhu da kungiyar.

Ya ce, ASUU ta ki janye yajin aikin ne saboda bukatarta ta a biya malaman jami’a albashin lokacin da suka yi cikin yajin aikin, bukatar da ministan ya yi watsi da ita.

Sai dai kuma ya ce, an warware wasu batutuwa da Kungiyar ke bukata.

Adamu, ya ce hudu daga cikin biyar na manyan makarantun kasar nan sun amince su janye yajin aikin nan da mako guda.

Ya kuma jaddada cewa za a iya bayyana irin wannan mataki ne bayan ganawa da shugabanninsu.